Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,005 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a. Sannan kuma mutum 24 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum – 204, Kwara-155, Oyo-124, Filato-80, FCT-75, Edo-56, Osun-48, Ondo-41, Kaduna-40, Rivers-40, Taraba-35, Borno-32, Ekiti-21, Ogun-20, Kano-14, Bayelsa-8, Delta-7, Bauchi-3 da Jigawa-2
Yanzu mutum 144,521 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 118,866 sun warke, 1,734 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 23,921 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Alhamis, mutum 938 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Filato, Benue, Katsina da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –52,722, FCT–18,366, Filato –8,647, Kaduna–8,025, Oyo–6,248, Rivers–5,953, Edo–4,217, Ogun–3,666, Kano–3,454, Delta–2,458, Ondo–2,604, Katsina–1,972, Enugu–1,829, Kwara–2,437, Gombe–1,891, Nasarawa–2,021, Ebonyi–1,646, Osun–2,065, Abia–1,338, Bauchi–1,195, Borno-1,138, Imo–1,283, Sokoto – 763, Benue- 1,022, Akwa Ibom–1,253, Bayelsa 718, Niger–867, Adamawa–725, Anambra–1,271, Ekiti–677, Jigawa 488, Taraba 584, Kebbi 276, Yobe-250, Cross River–232, Zamfara 215, Kogi–5.