Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 506 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi Sannan kuma mutum 20 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum–22, Ondo-90, Kwara-89, Rivers-53, Borno-45, Gombe-32, FCT-28, Imo-26, Ogun-25, Kaduna-14, Kano-14, Edo-13, Osun-11, Cross River-10, Yobe-9, Ekiti-7, Kebbi-6, Nasarawa-6, Oyo-5 da Jigawa-1
Yanzu mutum 139,748 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 113,525 sun warke, 1,667 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,556 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Asabar, mutum 1,588 suka kamu a Najeriya, jihohin Anambra, Oyo, Kano, Gombe da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –51,685, FCT–17,824, Filato –8,297, Kaduna–7,818, Oyo–5,905, Rivers–5,759, Edo–4,006, Ogun–3,578, Kano–3,314, Delta–2,396, Ondo–2,506, Katsina–1,901, Enugu–1,829, Kwara–2,158, Gombe–1,802, Nasarawa–1,976, Ebonyi–1,540, Osun–1,805, Abia–1,338, Bauchi–1,164, Borno-1,085, Imo–1,220, Sokoto – 759, Benue- 917, Akwa Ibom–1,090, Bayelsa 695, Niger–847, Adamawa–673, Anambra–1,271, Ekiti–641, Jigawa 485, Taraba 496, Kebbi 276, Yobe-250, Cross River–222, Zamfara 215, Kogi–5.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce Najeriya za ta karbi kalaban ruwan maganin rigakafin Korona miliyan 16 ‘AstraZeneca’ a cikin Fabrairu.
Ya ce Najeriya za ta karbi maganin ‘AstraZeneca’ saboda karancin maganin kamfanin Pfizer da ake yi yanzu a fadin duniya.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce ta ƙafa asusun COVAX domin samar da maganin rigakafin korona wa kasashe ma su tasowa.
Zuwa yanzu COVAX ta tara kwalaben ruwan maganin Korona sama da biliyan daya kuma zai raba wa kasashe masu tasowa 92.
Asusun ta yi alkawarin samar da maganin rigakafin da zai isa duka kasashe masu akalla kashi 20% na muatanen.
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce dalilin da ya sa ake bata lokaci kafin a shigo da maganin rigakafin shine har yanzu masu hada maganin basu yanke shawaran lokacin da za su fara shigowa da maganin ba.
Duk da haka Najeriya za ta karbi kason farko na maganin rigakafin a Fabrairu.
Ehanire ya ce asusun da AU ta kafa AVATT ta yi alkawarin samar da kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona miliyan 41 wa Najeriya.
Ya ce da wannan magani da Najeriya za ta samu zai isa a yi wa akalla kashi 50% na mutanen kasar nan allurar.
Discussion about this post