Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,588 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar Sannan kuma mutum 6 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –535, Anambra-218, Oyo-155, FCT-150, Kano-124, Gombe-60, Kaduna-49, Ebonyi-48, Filato-46, Akwa Ibom-39, Niger-37, Edo-33, Katsina-23, Rivers-18, Taraba-15, Nasarawa-14, Ogun-11, Delta-9, Ekiti-2 da Jigawa-2
Yanzu mutum 139,242 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 112,557 sun warke, 1,647 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 25,038 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Juma’a, mutum 1,624 suka kamu a Najeriya, jihohin Osun, Akwa-ibom, Ondo, Nasarawa da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –51,663, FCT–17,796, Filato –8,297, Kaduna–7,804, Oyo–5,900, Rivers–5,706, Edo–3,993, Ogun–3,553, Kano–3,300, Delta–2,396, Ondo–2,416, Katsina–1,901, Enugu–1,829, Kwara–2,069, Gombe–1,770, Nasarawa–1,970, Ebonyi–1,540, Osun–1,794, Abia–1,338, Bauchi–1,164, Borno-1,040, Imo–1,194, Sokoto – 759, Benue- 917, Akwa Ibom–1,090, Bayelsa 695, Niger–847, Adamawa–673, Anambra–1,271, Ekiti–634, Jigawa 484, Taraba 496, Kebbi 270, Yobe-241, Cross River–212, Zamfara 215, Kogi–5.
Duba garin kiyaye dokokin Korona a Babban birnin Tarayya Abuja dake karkashin hukumar FCDA ta rufe wani asibiti da ke bada sakamakon gwajin Korona na karya.
Jami’an hukumar FCDA sun ce sun kama asibitin yana yi wa mutane gwajin Korona da basu sakamakon gwajin ba tare da izinin gwamnati ba.
Shugaban hukumar kuma wanda ya jagoranci tawagar askarawan Korona na ma’aikatar, Yakubu Mohammed ya ce asibitin na yi wa wadanda ke son fita zuwa kasashen waje gwajin Korona sannan ta basu sakamakon karya su kama gaban su.
Ya ce hukumar ta samu labarin aiyukan da asibitin ‘BMT Tourist Clinic and Diagnostic Centre’ dake Wuse II ke yi ne daga bakin ministan Abuja Muhammed Bello da kuma daga ofishin hukumar NCDC.
Jami’in yada labarai da wayar da kan mutane na hukumar Ihkaro Attah ya ce ofishin hukumar NCDC ce ta fara sanar da ministan Abuja karya dokar da asibitin ke yi.
A dalilin haka kuwa ministan Abuja ya ba da umarnin a binciki asibitin kuma a rufe ta nan take.
“Hukumar NCDC ta bai wa asibitocin da ta amince da su izinin yin gwajin cutar da bada sakamakon gwajin a kasar nan.
“Yana da mahimmancin mutane musamman wadanda ke bukatan tafiya zuwa kasashen waje su yi gwajin cutar a wadannan asibitoci.
Attah ya Yi Kira ga mutane da su guji yin gwajin cutar a asibitocin da ba a yardar musu su yi wannan gwaji ba.