Tunda aka shiga sabuwar shekarar 2021 Korona ta tsananta a Najeriya fiye da shekarar 2020, shekarar da cutar ta bullo a duniya.
Haka kuma mutuwa daga cutar ya karu matuka inda a jere a ake samu wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1340 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis. Sannan kuma mutum 14 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –275, FCT-320, Rivers-117, Oyo-100, Akwa Ibom-57, Ogun-51, Ebonyi-48, Benue-44, Adamawa-42, Imo-38, Kwara-35, Gombe-32,Kaduna-31, Edo-29, Osun-29, Kano-24, Ekiti-15, Katsina-14, Delta-13, Nasarawa-13, Jigawa-10 da Sokoto-3.
Yanzu mutum 136,059 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 110,449 sun warke, 1,632 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 23,978 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Laraba, mutum 1,138 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Kaon, Edo , Osun da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –50,593, FCT–17,563, Filato –8,068, Kaduna–7,737, Oyo–5,682, Rivers–5,636, Edo–3,891, Ogun–3,498, Kano–3,155, Delta–2,377, Ondo–2,339, Katsina–1,878, Enugu–1,829, Kwara–2,038, Gombe–1,710, Nasarawa–1,884, Ebonyi–1,492, Osun–1,725, Abia–1,323, Bauchi–1,164, Borno-1,009, Imo–1,194, Sokoto – 759, Benue- 892, Akwa Ibom–966, Bayelsa 688, Niger–789, Adamawa–673, Anambra–1,053, Ekiti–602, Jigawa 482, Taraba 433, Kebbi 270, Yobe-241, Cross River–212, Zamfara 209, Kogi–5.
Kwamitin PTF ta bayyana sunayen kananan hukumomi 22 dake jihohi 13 da Korona ta fi yi wa illa a kasar nan.
Shugaban sashen dake kula da ayyukan dakile yaduwar cututtuka na kwamitin PTF Mukhtar Muhammad ya ce an samu kashi 95% na mutanen da suka kamu da cutar a mafi yawan wadannan kananan hukumomi a cikin makonni shida da suka wuce.
Sakamakon gwajin Korona da ake yi ya nuna cewa mutum sama da 1000 ke kamuwa da cutar kusan kullum a makonni shida da suka gabata a kasar nan.
1. Jihar Enugu
Karamar hukumar Nkanu ta Yamma
2. Babban birnin tarayya Abuja
Abuja Municipal, Gwagwalada.
3. Jihar Gombe
Karamar hukumar Gombe
4. Jihar Kaduna
Kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Kudu
5. Jihar Kano
Karamar hukumar Nassarawa
6. Jihar Katsina
Karamar hukumar Katsina
7. Jihar Kwara
Kananan hukumomin Ilorin ta Kudu da Ilorin ta Yamma
8. Jihar Legas
Kananan hukumomin Eti-Osa, Ikeja, Kosofe da Lagos Mainland
9. Jihar Nasarawa
Kananan hukumomin Keffi da Lafia
10. Jihar Oyo
Karamar hukumar Ibadan ta Arewa
11. Jihar Filato
Kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu
12. Jihar Rivers
Karamar hukumar Port-Harcourt
Discussion about this post