KORONA BAIROS: Gwamnati ta rufe Kasuwannin Wuse da UTC na kwanaki uku

0

Mahukunta a babban birnin tarayya Abuja sun garkame shahararren kasuwar Wuse dake tsakiyar gari garin Abuja sabo take dokokin korona da mutane ke yi a kasuwar.

Baya ga kasuwar Wuse, gwamnati ta garkame katafaren kasuwra UTC dake Garki.

Babban dalilin da ya sa gwamnati ta garkame wadannan kasuwanni biyu kuwa shine saboda karya dokokin Korona da mutane ke yi.

Ƴan kasuwa da dama sun shaida wa wakilin mu cewa wannan hukunci da mahukunta a babban birnin tarayyar suka dauka yayi matukar tsauri. Ƴan kasuwan sun yi cincirindo a kofar shiga kasuwannin sun yi tagumi cikin damuwa.

Wani jami’in hukumar FCTA ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wannan hukunci da hukumar ta dauka ya zama dole kuma shine kawai mafita a gareta domin mutane suna yi wa dokokin kare kai daga kamuwa da Korona kunnen uwar shegu.

Za a rufe kasuwanni har na tsawon kwanaki uku.

Share.

game da Author