KORONA: An samu karin mutum 643 da suka kamu ranar Litini

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 643 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini Sannan kuma mutum 6 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum–86, Oyo-88, Rivers-55, Edo-54, Akwa Ibom-53, Adamawa-52, Filato-45, Kaduna-41, FCT-34, Kwara-27, Benue-20, Kano-19, Delta-18, Nasarawa-16, Niger-15, Bayelsa-11, Borno-5, Bauchi-2 da Sokoto-2.

Yanzu mutum 140,391 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 114,635 sun warke, 1,673 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,083 ke dauke da cutar a Najeriya.

Ranar Lahadi, mutum 506 suka kamu a Najeriya, jihohin Ondo, Kwara, Rivers, Barno da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –51,771, FCT–17,858, Filato –8,342, Kaduna–7,859, Oyo–5,993, Rivers–5,814, Edo–4,060, Ogun–3,578, Kano–3,333, Delta–2,414, Ondo–2,506, Katsina–1,901, Enugu–1,829, Kwara–2,185, Gombe–1,802, Nasarawa–1,992, Ebonyi–1,540, Osun–1,805, Abia–1,338, Bauchi–1,166, Borno-1,090, Imo–1,220, Sokoto – 761, Benue- 937, Akwa Ibom–1,143, Bayelsa 706, Niger–862, Adamawa–725, Anambra–1,271, Ekiti–641, Jigawa 485, Taraba 496, Kebbi 276, Yobe-250, Cross River–222, Zamfara 215, Kogi–5.

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga gwamnatin da ta fadada kamfen din wayar da kan mutane game da allurar rigakafin cutar korona da za a shigo da su a watan Faburairu.

Sa’ad ya ce yin haka zai taimaka wajen kawar da rudanin da rashin yarda a tsakanin mutane wanda shine yanzu ya karade gari.

Sultan ya kara da cewa lallai fa yana kira ga gwamnati ta maida hankali wajen wayar da kan mutane domin a gari rudani ake yadawa cewa wai maganin an kirkiro shi domin a kashe mutanen Afrika.

“Mutane na yada labaran cewa rigakafin korona gubace kuma anyi ta ne don a kashe mutane Afrika. Amma kada mu manta cewa tun ba yau ake shigo da magunguna daga kasashen waje sannan idan ma ana so a kashe mu din ne ai akwai hanyoyi da dama da za a iya bi ba sai ta rigakafin Korona ba.

“Yin allurar rigakafin korona kyauta ne amma amincewa da yin allurar ya rage ga mutanen kasa.

Share.

game da Author