Mako daya kadai bayan sama da kwalbar allurar rigakafin korona na AstraZeneca-Oxford ya isa Afrika ta Kudu, mahukuntan kasar sun dakatar da gwajin allurar saboda ta kasa hana wadanda aka yi zakaran-gwajin-dafi da su kamuwa daga rashin lafiya.
Mahukuntan sun ce wadanda aka yi wa gwajin sun kasa samun makaran hana kamuwa daga cutar korona mai zafi, mafi saurin kisa, wato ‘Covid-19 variant’. Ko kuma B.1.351 a takaice.
Ministan Lafiya na Afrika ta Kudu, Zweli Mkhie ya bayyana cewa gwajin allurar rigakafin da aka yi a Jami’ar Witwatersrand ya nuna AstraZeneca cewa ya rage kwayoyin kamuwa da cutar korona da kashi 22% bisa kashi 100% kacal.
“Dalili kenan za mu dakatar da gwajin allurar rigakafin AstraZeneca domin mu sake nazarin tasiri ko rashin tasirin ta a jikin wadanda su ka kamu da cuta bayan an dirka masu wa rigakafin allurar.
“Za mu dakata har sai masana ilmin kimiyya sun ba mu shawarar da za mu dauka a mataki na gaba.” Inji Ministan Lafiyar Afrika ta Kudu, a ranar Lahadi.
Yayin da Afrika ta Kudu ta dakatar da gwajin allurar rigakafin AstraZeneca, ita kuwa Najeriya ta na jiran isowar kwalaben wannan ruwan allurar har guda milyan 16 kafin karshen watan Fabrairu.
Har yanzu dai ba a samu rahoton mutuwar ko da mutum daya daga cikin mutane 2,000 din da aka yi wa gwajin rigakafin korona na ruwan allurar AstraZeneca ba.
Wadanda aka yi wa gwajin dai akasari bas u wuce shekaru 31 ba.
Sai dai kuma kamfanin allurar AstraZeneca ya bayyana a cikin jaridar New York Times cewa gwajin bai yi wa rigakafin adalci ba, domin akasarin wadanda aka yi wa gwajin duk masu shekaru 31 ne ko wadanda ba su wuce ba.
Kenan a ra’ayi ko matsayar kamfanin, yawancin wadanda aka yi wa gwajin ba masu shekaru da yawa ba ne.
Masu wadannan shekaru a cewar kamfanin ba za su zama ma’aunin gamegari na tabbatar da sahihancin AstraZeneca ba.
A Najeriya ma an tabbatar da bullar sabuwar korona mai zafi da saurin kisa, wato Covid-19 varient, ko kuma B.1.351.