Kungiyar Gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa rikicin da faru a Kasuwar Shasha (Sasa) a Ibadan ta jIhar Oyo, inda aka kashe Hausawa aka kone dukiyoyin su, ba rikicin kabilanci ba ne.
Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Bagudu ne ya yi wannan sanarwa a madadin sauran gwamnonin Najeriya, bayan sun kai ziyarar gani da ido a inda rikicin ya afku.
“Kawai dai sharrin wasu ’yan iska ne wadanda su ka kitsa rikicin domin kawai su kwashi dukiyar mutane kuma su tayar da fitina.”
PREMIUM TIMES ta buga cikakken bayanin yadda aka yi asarar mutane da yawa, kuma aka kone dukiyoyin jama’a, musamman Hausawa a kasuwa da unguwar Shasha a Karamar Hukumar Akinyele, jihar Oyo.
Bagudu ya yi wannan jawabi a daidai lokacin da ake ci gaba da watsa bidiyon yadda ake bin Hausawa a guje ana duka da kisa.
Sannan kuma an nuno dubban su wadanda su ka yi gudun hijira su ka boye gidan Sarkin Hausawan Sasa, Haruna Maiyasin.
A daya bangaren kuma, yayin da Gwamnonin Arewa ke cewa ba rikicin kabilanci ba ne, dubban Hausawa na ci gaba da kowama yankin Arewa, gudun kada a kara afka masu da kisa.
Wadanda su ka raka Gwamna Bagudu sun hada da Abdullahi Ganduje na Kano, Abubakar Bello na Neja, Bello Matawalle na Zamfara.
‘A Daina Cewa Rikicin Oyo Na Kabianci’ Ne –Gwamna Bagudu
Gwamna Bagudu ya roki matasa da dakarun soshiyal midiya su daina fassara rikicin kisan Hausawa a Oyo a matsayin rikicin kabilanci.
Ya kuma ja hankalin su a daina ruruta wutar rikici soshiyal midiya don kada a haddasa fitina a kasar nan.
“Dama irin wannan rikicin kan faru a cikin al’umma, amma wani lokacin wasu ’yan iska ne ke amfani da rikicin su kwashi kayan jama’a kuma su haddasa hargitsi.
“Mun gani da idon mu irin barnar da aka yi a Kasuwar Shasha. Amma abu mafi tayar da hankula shi ne rayukan da aka rasa. Mun yi tir da wannan kisa da aka yi.”
Bagudu ya ce dama can akwai rashin jituwa kan shugabancin kasuwar Shasha, to kuma jama’a dama kadan su ke jira sai su tayar da fitina.
Gwamnonin sun ziyarci Baale na Shasha Akinlade Ajani da kuma Sarkin Hausawa na Shasha, Haruna Maiyasin.
Sun yi kira da a ci gaba da zaunawa lafiya da juna.