Kiris ya rage wa Najeriya ta tarwatse – Manyan Limaman Katolika

0

Najeriya “ta kama hanyar tarwatsewa, kuma kiris kawai ya rage ta karasa zangon da ba mai iya hana ta tarwatsewar. Don haka wajibin kowane dan kasar nan ne ya tashi tatsaye domin ya hana afkuwar wannan mummunan al’mari.”

Sanarwar Hadaddiyar Kungiyar Limaman Darikar Katollika kenan dangane da yadda matsalar tsaro ke kara muni a Najeriya.

“Tubulan da aka gina Najeriya sai rugujewa su ke yi, abin takaici ana ji ana gani, amma an kasa hana wannan katanga ci gaba da rugujewa. Kashe-kashe sun yi yawa a fadin kasar nan.

“Wadanda mulki ke hannun su kuma ko dai ba su iya shawo kan lamarin, ko kuma da gangan sun ki magance matsalar.”

Cikin wata sanarwa da Shugaba da Sakataren Hadaddiyar Kungiyar Manyan Limaman Katolika, Agustine Akubeze da Camilus Raymond Umoh su ka sa wa hannu, sun bayyana cewa lokaci fa ya kusa kure wa Najeriya, idan ba a tashi da gaggawa an shawo kan matsalar tsaro ba.

Sun yi wannan gargadi makonni biyu bayan satar dalibai da iyalai a Sakandaren Kimiyya ta garin Kagara, da ke cikin Karamar Hukumar Rafi, a Jihar Neja.

Bishop-Bishop din sun nuna damuwa sosai yadda kalubale sai karuwa ya ke yi a kullum cikin sassan kasar nan, amma gwamnati ta kasa yin komai.

Dalilin wannan sakaci ne na hukuma inji kungiyar ta Bishop-Bishop din Darikar Katolika har aka yi sakaci wasu takadarai su ka bayyana masu ruruta wutar kabilanci a kasar nan.

Wannan gargadi ya zo ne bayan kwanakin baya tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ya nuna Najeriya ta kusa tarwatsewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.

PREMIUM IMES ta buga labarin da Abdulsalami Abubakar ya ce Najeriya ta kama hanyar tarwatsewa gadan-gadan.

Rahoton ya nuna cewa Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, ya yi kakkausan gargadin cewa idan ba a gaggauta dakile hargitsi da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a fadin kasar nan daban-daban ba, to Najeriya za ta iya tarwatsewa ba da dadewa ba.

Haka Abdulsalami ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba, a Minna, babban birnin jihar Neja.

Wannan gargadi na shi ya zo ne kwanaki kadan bayan da aka kashe wasu Hausawa a Kasuwar Shasha da ke jihar Oyo.

Duk da dai Hausawa ne zalla aka kashe kuma aka kona masu dukiya, a fadan da ake kallo na kabilanci ne, su kuma Gwamnonin Najeriya a ta bakin Gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu, sun ce ba fadan kabilanci ba ne.

Haka kuma a cikin makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Bauchi da na Benuwai su ka yi zazzafar cacar-baki dangane da batun tsaro a kasar nan.

Yayin da gwamnan Benuwai ke kira da a bai wa kowane dan Najeriya dama da iznin mallakar bindigar kare kan sa, shi ma Gwamnan Buchi Bala Mohammed cewa ya yi tilas ce ta sa Fulani makiyaya su ke mallakar bindigogi, saboda kashe su da ake yi ana sace masu shanun su.

Shi kuwa Samuel Ortom na Benuwai, fata-fata ya yi da Bala na Bauchi, ya ce rashin hankali har wani ya fito ya goyi bayan daukar bindigogi da Fulani makiyaya ke yi.

Abubakar, wanda tsohon Janar ne na soja, ya bayyana cewa rigingimun da ke faruwa kwanan nan a sassa daban-daban na kasar nan, idan ba a yi hattara ba, to za su iya haddasa tarwatsewar kasar nan.

“Matsawar ba a gaggauta shawo kan wadannan fitintinu ba, to fa Najeriya na iya tarwatsewar da sake hade ta bai zai taba yiwuwa ba.”

Daga nan sai ya yi kira ga ’yan Najeriya musamman gwamnnonin jihohi 36 na kasar nan, “su dauki nauyin dannewa da taushe muryoyin duk wasu masu karajin tayar da zaune tsaye a yankunan su.

“Saboda irin wadannan muryoyin ne ke ingiza-mai-kantu-ruwa, su na zuga matasa ana hargitsi da kashe-kashen da ka iya tarwatsa kasar nan baki daya.

Ya hori gwamnoni su hada kai, kuma su mutunta ra’ayoyin kowanen su, tunda babu yadda za a yi ra’ayin wannan ya yi daidai da na wannan a wasu mas’aloli.

Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalami, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya na Najeriya, ya sake jaddada gargadin sa cewa hadin kai ne kadai zai iya cetar kasar nan daga tarwatsewa.

“Idan aka bari wannan ’yan ta’adda da masu garkuwa da ashi da makami da kuma abubuwan da ke faruwa a wasu sassan kasar nan su ka ci gaba da muni, musamman hare-haren kabilanci, to fa an kusa danganawa cikin ramin da kowa ke son kasar nan ta afka ciki ba.

“To mu dai a matsayin mu na Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa, mu na kara yin kira da jan hankali da babbar murya ga milyoyin ’yan Najeriya cewa a hakura haka nan a zauna lafiya.

“Saboda sai an hada hannu bibbiyu za a iya ciccibar kasar nan daga halin da ta ke a fitar da ita cikin mawuyacin halin da ta afka, tun kafin a yi sakacin da zai iya janyo tarwatsewar ta.”

“Jama’a na cikin mahuyacin hali a kasar nan. Dubban jama’a a gudun hijira a sansanoni daban-daban a yankuna da garuruwan kasar nan. Da dama sun rasa gidajen su da gonaki da sauran dukiya. Banda ma batun dimbin mutanen da ke rasa rayukan su.

“Mun ga irin yadda manoma su ka sha wahalar yadda za su yi noma da kuma girbe amfanin gonar su a shekarar da ta gabata. To idan kuwa aka yi la’akari da halin da ake ciki a yanzu, lamarin zai kara muni a wannan shekarar damina da kaka mai zuwa.”

Share.

game da Author