Kakudubar dambarwa ta tirnike a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, a ranar Alhamis, yayin da lauyan Faisal Maina ya karyata ikirarin da lauyan EFCC ya yi, inda ya shaida wa kotun cewa Faisal ya tsere Amurka.
Bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda lauyan EFCC ya ce wa kotu Faisal ya tsere Amurka, Mai Shari’a Okon Abang ya umarci kotu ta rike kudin ajiya ko kadarar mai belin sa, Dan Majalisar Tarayya, Sani Dangaladima.
Sai dai kuma baya ta haihu, yayin da lauyan Faisal mai suna Anayo Adibe ya shaida wa kotu cewa karya EFCC ke yi, Faisal ya na hannun ‘yan sanda a Sokoto.
Bayan Mai Shari’a ya saurari bangarorin biyu, ya bayyana cewa “to ni kun raba min hankali, na rasa wanda zan yarda da maganar sa.”
Shi kan sa mai shari’ar ya ce shi ma ya ji an ce an kama Faisal a Sokoto.
Sai dai kuma lauyan EFCC ya ce labarin kama Faisal a Sokoto duk ji-ta-ji-ta ce.
Lauyan Faisal mai suna Anayo Adibe, ya shaida wa kotu cewa ya sanar da kotun a ba tun a ranar ba cewa an kama Faisal a Sokoto.
Ya ce shi kan sa Faisal din ya kira shi ya sanar da shi cewa an kama shi a Sokoto. Kuma ya yi kokarin ganin Faisal din, amma abin bai yiwu ba.
“Shi da kan sa Faisal din ya kira ni ya ce min ‘yan sanda sun kama shi a Sokoto. Tun daga nan kuma na yi ta kokarin samun lambar wayar sa, amma ta na kashe.” Inji lauyan sa.
“Kuma har yanzu Rundunar ‘Yan Sanda ta ki fitar da bayanin halin da su ke ciki da Faisal, duk kuwa da kokarin da na yi don ganin sa.
“Saboda haka maganar ma a ce wai Faisal ya gudu Amurka, tatsuniya ce kawai.”
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Hukumar EFCC ta shaida wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja cewa Faisal dan Abdulrashid Maina, wanda ake tuhuma a kotu tare da mahaiin na sa, ya gudu zuwa Amurka.
Lauyan EFCC mai suna Mohammed Abubakar, kuma wanda ya shigar da karar a madadin EFCC, ya ce Faisal ya tsere, a daidai lokacin wa kotun ke tuhumar sa da laifukan harkallar karkatar da kudade har tuhumomi uku, shi da mahaifin sa.
Lauyan ya ce EFCC ta samu labarin cewa Faisal ya tsere zuwa Amurka, inda ya bi ta kan iyakar Jamhuriyar Nijar.
Kafin haka dai a ranar Alhamis sai da Mai Shari’a Okon Agbang ya umarci Dan Majalisar Tarayya, Sani Dangaladima, wanda ya karbi belin Faisal cewa ya damka wa kotun kadarorin sa da ya jingina wa kotun a matsayin sharadin karba belin Faisals.
Shi dai Dangaladima, wanda shi ke wakiltar Karamar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara, ya rattaba amincewar karbar belin Faisal kan kudi naira milyan 60.
Shi ma Maina sai da ya yi kokarin tserewa zuwa Amurka, amma aka damke shi a cikin Jamhuriyar Nijar.
A halin yanzu EFCC ta ki amincewa da sake bada belin Maina, saboda ya na da katin zama dan kasar Amurka.
Ta ce tunda ya yi kokarin gudu a watannin baya, a yanzu ma idan aka bayar da belin sa, sake gudu zuwa Amurka zai yi.