KARYA DOKAR KORONA: kwamitin PTF ta soke fasfo din matafiya 100 da suka shigo kasar nan

0

Kwamitin dakile yaduwar cutar Korona ta ƙasa PTF ta soke fasfo din matafiya 100 da suka shigo kasar nan.

Kwamitin ta yi haka ne saboda karya dokar dakile yaduwar korona da wadannan matafiya suka yi bayan sun shigo kasar nan.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya kwamitin ta kafa dokar dakile yaduwar korona wanda ya kamata duk wani matafiyi ya kiyaye.

Killace kai na tsawon kwanaki bakwai da maimaita gwajin cutar bayan kwanaki bakwai da shigowa kasar nan na daga cikin dokokin da ya kamata a kiyaye.

A ranar Talata Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce za a buga sunaye da sauran bayanai game da fasfo din mutanen da suka karya dokar korona a shafin kwamitin na tiwita dake yanar gizo.

Mustapha ya ce yin haka zai zama darasi ga duk wanda zai shigo kasar nan ba tare da ya kiyaye bin dokar Korona ba.

Gwamnatin Najeriya ta hana matafiyaficewa daga Kasar nan tun daga 5 ga Fabrairu zuwa 39 ga Yuli.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 643 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini Sannan kuma mutum 6 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum–86, Oyo-88, Rivers-55, Edo-54, Akwa Ibom-53, Adamawa-52, Filato-45, Kaduna-41, FCT-34, Kwara-27, Benue-20, Kano-19, Delta-18, Nasarawa-16, Niger-15, Bayelsa-11, Borno-5, Bauchi-2 da Sokoto-2.

Yanzu mutum 140,391 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 114,635 sun warke, 1,673 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,083 ke dauke da cutar a Najeriya.

Ranar Lahadi, mutum 506 suka kamu a Najeriya, jihohin Ondo, Kwara, Rivers, Barno da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –51,771, FCT–17,858, Filato –8,342, Kaduna–7,859, Oyo–5,993, Rivers–5,814, Edo–4,060, Ogun–3,578, Kano–3,333, Delta–2,414, Ondo–2,506, Katsina–1,901, Enugu–1,829, Kwara–2,185, Gombe–1,802, Nasarawa–1,992, Ebonyi–1,540, Osun–1,805, Abia–1,338, Bauchi–1,166, Borno-1,090, Imo–1,220, Sokoto – 761, Benue- 937, Akwa Ibom–1,143, Bayelsa 706, Niger–862, Adamawa–725, Anambra–1,271, Ekiti–641, Jigawa 485, Taraba 496, Kebbi 276, Yobe-250, Cross River–222, Zamfara 215, Kogi–5.

Share.

game da Author