KADUNA: ‘Yan bindiga sun kashe mutum 14 a Birnin Gwari, 5 a Kajuru ranar Lahadi

0

Mahara dauke da manyan bindigogi sun kashe akalla mutum 14 a kauyen Tashar Kadanya dake Kushemiki karamar hukumar Birnin Gwari ranar Asabar.

Wani mazaunin wannan kauye Bashir Lawal ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa mahara sun dira garin Tashar Kadanya ne adaidai mutane na shirin sallar Magriba.

” Muna zaune sai muka ji ana harbin bindiga ta ko ina, daga nan ne fa muka arce cikin daji. Maharan sun zo a bisa babura inda suka rika farfasa shaguna suna dirka wa duk wanda suka gani harsashi.

” Sai da suka yi kusan awa biyu sun barna akafin nan suka fice daga kauyen Tashar Kadanya. Bayan haka jami’an tsaro sun isa wannan wuri daga baya kuma suka tafi.

Lawal ya ce an kashe mutane da dama sannan wasu da dama suna asibiti ana kula da su.

” Bayan kisa da suka yi sun farfasa shaguna sun kwashi na kwasa kafin suka arce cikin daji.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, shaida cewa mutum 14 ne zuwa yanzu aka tabbatar da rasuwar su bayan aika-aikan da yan bindiga suka yi a Birnin Gwari.

Sannan kuma ya bada suna yen su kamar haka:

Malan Sani Barume
Yahaya Bello
Amadu Dan Korau
Samaila Niga
Jamilu Haruna
Lawal Majiya
Dan Malam Rabo
Dauda Kafinta
Hassan Mai Makani
Bashir Haruna
Lawal Ali
Mu’azu Haruna
Mai Unguwa Sa’adu
Harisu Bako

Harin Kajuru

A kauyen Kujeni, karamar hukumar Kajuru, mahara sun kashe akalla mutum biyar sannan sun cinna wa wuraren ajiye abinci da kayan gini, sun kona gidajen mutane da kuma wani coci.

Wadanda suka kashe sun hada da:

Bulus Jatau
Hanatu Emmanuel
Bitrus Tuna
Yohanna Mika
Monday Ayuba

Sannan kuma Bulus Sambayi da Godwin Yakubu sun samu rauni.

Kwamishina Aruwan ya ce tuni gwamnati ta aika da kayan agaji ga wadanda wadanda wannan tashin hankali ya afka wa.

” Sannan kuma gwamna Nasir El-Rufai ya mika jajen sa ga wadanda wannan mummunar abu ya afka wa yana mai cewa gwamnati za ta cigaba da kokarin ganin an kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

Share.

game da Author