Kadan ya rage Jonathan ya sauke ni daga kujerar minista don na baiwa jami’ar Baze fili a Abuja – Gwamna Bala

0

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammed ya bayyana cewa kaɗan ya rage da ya rasa mukamin ministan Abuja a lokacin mulkin Goodluck Jonathan don ya baiwa shugaba kuma mai mallakin jami’ar Baze , Yusuf Baba-Ahmed fili ya gina jami’ar.

Gwamna Bala ya shaida haka ne da yake karbar bakuntar shugaban jami’ar da ya kai masa ziyayar a garin Bauchi, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

” Dukkan ku kun san alaka ta da jami’ar Baze da kuma gwagwarmayar da aka yi. Wata ta so dole ita ce za a ba wannan fili da karfin tsiya amma na tsaya tsayin daka don ganin sai Baze ta samu mallakin wannan fili. Ba ku san haka ba amma yanzu ina gaya muku dambarwar da aka yi wajen tabbatar da Baze ta samu mallakin wannan fili.

” Ina farin ciki da alaka ta da wannan makaranta kuma ina maraba da ku. Bayan haka ina so ku sani cewa jami’ar  sananniya ce a duniya baki ɗaya kuma na yi matukar farin ciki da na ga ana tallarta jami’ar Baze a tashar CNN a talabijin.

A karshe gwamna Bala ya ce yayi murna da maraba da guraben karatu da jami’ar ta kebe wa ƴan asalin jihar Bauchi da kuma tallafin karatu  na kashi 75 bisa 100 kudin makaranta da ta rage wa ƴan asalin jihar.

Gwamna Bala ya umarci kwamishinan ilmin jihar Aliyu Tilde ya yayi amfani da wannan dama wajen tura ƴara ƴan asalin jihar Bauchi karatu a wannan jami’a.

A wannan ziyara shugaban jami’ar, Baba-Ahmed ya jinjina wa gwamna Bala sannan ya gode masa bisa gudunmawar da ya ke ba jami’ar tun da aka kafata har zuwa yanzu.

Share.

game da Author