Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Kasa na Jam’iyyar APC, Yekini Nabena, ya caccaki Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed dangane da kiran da ya yi na a soke aikin sabunta rajista a Jihar Kwara a sake sabon aikin sabunata rajistar shiga jam’iyyar a jihar Kwara.
Nabena ya shawarci Lai cewa ya kaddara shi ne Gwamnan Kwara idan shi ne ya zai yi. Saboda haka idan har ya na so a yi masa biyayya, to tilas shi ma sai ya bi na sama da shi a siyasar jihar Kwara.
PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin yadda Lai Mohammed ya kira taron manema labarai, ya nemi a soke aikin sabunta rajistar shiga ko ci gaba da zama dan jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Kwara, inda ya bayyana cewa an yi wa bangaren magoya bayan sa rashin adalci, kuma ba a gudanar da aikin kamar yadda dokar jam’iyya ta shimfida ba.
Lai ya zargi shugaban kwamitin aikin sabunta rajista a Jihar Kwara, John Danboi da yin rashin adalci da nuna bangarancin fifita bangaren Gwamna AbdulRazak na Jihar Kwara.
Ministan y ace Danboi ya dauki bangaren Gwamna AbdulRazak a jihar Kwara, inda a halin yanzu jam’iyyar APC a jihar ta rasbu guda hudu.
Nabena ya ce ya na mamaki babban mutum kamar Lai Mohammed wand aba zaune ya ke a Jihar Kwara ba, ya rika zaunawa a Abuja wasu na kai masa rahotanni karairayi, shi kuma ya na gaskatawa.
Martanin Lai Mohammed
A martani da Lai Mohammed ya maida wa Nabena ranar Talata, ya ce bashi da hurumin yayi magana da yawun APC domin tun bayan rusa kwamitin gudanarwar Jam’iyyar, ba a nada wani mai magana da yawun jam’iyyar ba. Saboda haka shi dai Nabena yana sururun sa ne kawai.
” Babu wani da muka sani wai kakakin jam’iyyar APC, domin ba a nada wani kakaki ba tun bayan rusa kwamitin gudanarwar jam’iyyar da aka yia bara. Nabena na surutun sa ne kawai.” In ji Lai.