Jihohi 26 Wadanda Kamfanonin Zuba Jari Ko Daya Ba Su Zuba Jari Ba A 2020 – NBS

0

Jihohi 26 daga cikin jihohi 36 da Abuja da ke kasar nan, sun kasa samun ko da wani kamani daya tilo da ya amince ya zuba jari a cikin su a shekarar 2020 ba.

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ce ta fitar da jerin sunayen a ranar Litinin.

Rohoton ya nuna jihohi 10 kadai sai fa Abuja ne kamfanonin zuba jari su ka albarkace su a cikin 2020.

Wani rahoto ne dai da babban bankin Najeriya CBN ya tattara yawa da adadin zunzurutun jarin da baki daga kamanonin kasashen waje su ka shigo su ka zuba a cikin 2020.

NBS ne ya fitar da kididdigar bayanan a ranar Juma’a.

Sai dai rahoton ya nuna cewa daga cikin dalilan faruwar hakan, akwai bullar cutar korona, wadda ta gurgunta komai a cikin shekarar 2020.

An samu ragin kudaden zuba jari a cikin kasar nan a cikin 2020. Domin dala bilyan 9.7 kacal masu zuba jari daga waje su ka zuba cikin 2020. Sabanin 20219 da aka zuba har dala bilyan 24.

Hakan na nuni da cewa an samu gibi ko ragin kashi 59.7 kenan tsakanin 2019 da 2020.

Jihohi 10 Da Kamfanonin Waje Su Ka Zuba Wa Jari Cikin 2020:

Jihar Lagos an zuba mata dala bilyan $8.3, Abuja mai dala bilyan $1.3.

Sauran sun hada da Abia mai dala milyan $56, Niger dala milyan $16.4, Ogun dala milyan $13.4.

Anambra dala milyan $10.2 million, Kaduna dala milyan $4.03, Sokoto dala milyan $2.5 da Kano dala milyan $2.4 kacal.

Akwa Ibom dala milyan $1.05 sai Adamawa dala $20,000 kacal.

Jihohi 26 Da Ba A Zuba Wa Ko Kwandala Ba:

Sun hada da jihohin Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Nasarawa, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Taraba, Yobe da Zamfara.

Share.

game da Author