Jerin Sunayen Kungiyoyin Da Ke Kira Ga Buhari Ya Sauka Ko A Tsige Shi, Tare Da Dalilan su

0

Yawan kashe-kashe babu kakkautawa a fadin kasar nan, yayin da gwamnati ta kasa yin komai, har ta kai don lalacewa MinistanTsaro ya ce jama’a su daina jin tsoro, su fito su tunkari masu kashe su kawai, wato kowa ta sa ta fisshe shi, ya kare kan sa idan zai iya.

Garkuwa da mutanen da ake yi a Najeriya, ya yi munin da ba a taba ganin irin wannan bala’in a kowace kasa a Afrika ba.

Yara ‘yan makaranta babu sauran kwanciyar hankali a fadin kasar nan, saboda su da ikyayen su kullum ana zaman zullumin masu garkuwa da mutane, wadanda ba su jin tausayin kama kananan yara.

Mun yi Allah-wadai da tsarin Gwamnatin Tarayya, wanda ta ke kwasar makudan kudaden talakawa ta na biyan ‘yan ta’adda, inda a waje daya ta na kara ruruta karfin ta’addanci a kasar nan.

● Har yanzu babu alamun kawo karshen Boko Haram a Arewa maso Gabas, an bar sojojin mu kullum cikin jidali.

● Tantagaryar rashin adalcin gwamatanin Buhari, wadda ta daure wa jami’an tsaro gindi su na jijjibgar masu dauke da kwalaye su na zanga-zanga. A waje daya kuma masu kashe jama’a, masu fyade da masu garkuwa a Najeriya har su na kama mata da kananan yara, su gwamnatin Buhari ke dumbuza wa makudan kudade da sunan ‘afuwa’.

Wannan tantafaryar daure wa ta’addanci gindi ne a doron kasa a ce wai masu kashe mana sojoji kuma su ake ja a jika ana ba su kudade bayan an yi masu afuwa.

● Akwai kuma gagarimar matsalar yadda makiyaya ke kashe manoma, sai yadda manoman ke yin kisan ramuwar gayya, saboda gwamnati ta kasa yin komai.

Sunayen Kungiyoyi 44:

1. Centre for Democracy and Development (CDD)

2. Centre for Democratic Research and Training (CRDDERT)

3.Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC)

4. Media Rights Agenda (MRA)

5. Centre for Information Technology and Development (CITAD)

6. Socio-Economic Right and Accountability Project (SERAP)

7. Zero-Corruption Coalition (ZCC)

8. Partners on Electoral Reform

9. African Centre for Media and Information Literacy (AFRICMIL)

10. National Procurement Watch Platform

11. Praxis Center

12. Resource Centre for Human Rights and Civil Education (CHRICED)

13. Social Action

14. Community Action for Popular Participation

15. Borno Coalition for Democracy and Progress (BOCODEP)

16. Global Rights

17. Alliance for Credible Elections (ACE)

18. Youth Initiative for Advocacy, Growth & Advancement (YIAGA)

19. Tax Justice and Governance Platform

20. Environmental Rights Action/Friends of the Earth, Nigeria

21. Women In Nigeria

22. African Centre for Leadership, Strategy & Development (Centre LSD)

23. Rule of Law and Accountability Advocacy Centre(RULAAC)

24. Women Advocate Research And Documentation Centre

25. Community Life Project

26. Nigerian Feminist Forum

27. Alliances for Africa

28. Spaces for Change

29. Nigerian Women Trust Fund

30. Corporate Accountability and Public Participation Africa

31. BudgiT Foundation

32. State of the Union (SOTU)

33. Action International Nigeria

34. Femi Falana Chamber

35. HEDA Resource Centre

36. Conscience for Human Rights and Conflict Resolution

37. Organization Community Civic Engagement(OCCEN)

38. Say NO Campaign—Nigeria

39. Women In Media

40. Health of Mother Earth Foundation (HOMEF)

41. Sesor Empowerment Foundation

42. House of Justice

43. Molluma Medico-Legal Center

44. Open Bar Initiative

Share.

game da Author