Jerin Kananan hukumomi 22 da Korona ta fi yi wa Illa a Najeriya

0

Kwamitin PTF ta bayyana sunayen kananan hukumomi 22 dake jihohi 13 da Korona ta fi yi wa illa a kasar nan.

Shugaban sashen dake kula da ayyukan dakile yaduwar cututtuka na kwamitin PTF Mukhtar Muhammad ya sanar da haka ranar Litini.

Muhammad ya ce an samu kashi 95% na mutanen da suka kamu da cutar a mafi yawan wadannan kananan hukumomi a cikin makonni shida da suka wuce.

Sakamakon gwajin Korona da ake yi ya nuna cewa mutum sama da 1000 ke kamuwa da cutar kusan kullum a makonni shida da suka gabata a kasar nan.

1. Jihar Enugu
Karamar hukumar Nkanu ta Yamma

2. Babban birnin tarayya Abuja
Abuja Municipal, Gwagwalada.

3. Jihar Gombe
Karamar hukumar Gombe

4. Jihar Kaduna
Kananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Kudu

5. Jihar Kano
Karamar hukumar Nassarawa

6. Jihar Katsina
Karamar hukumar Katsina

7. Jihar Kwara
Kananan hukumomin Ilorin ta Kudu da Ilorin ta Yamma

8. Jihar Legas
Kananan hukumomin Eti-Osa, Ikeja, Kosofe da Lagos Mainland

9. Jihar Nasarawa
Kananan hukumomin Keffi da Lafia

10. Jihar Oyo
Karamar hukumar Ibadan ta Arewa

11. Jihar Filato
Kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu

12. Jihar Rivers
Karamar hukumar Port-Harcourt

13. Jihar Sokoto
Karamar hukumar Wamako

Haka nan kuma Muhammad ya kara da cewa yin gwajin cutar na cikin hanyoyin dake taimakawa wajen sanin matsayin fantsamar cutar domin daukan matakin da ya kamata wajen rage yaduwar cutar.

Muhammad ya ce jihohin Yobe, Jigawa, Zamfara da Kebbi na daga cikin jihohin da ba su yin gwajin cutar yadda ya kamata. Ita ko Jihar Kogi ba a maganan ta kwata-kwata.

Share.

game da Author