Jami’an tsaro sun ceto wasu matafiya 13 da Boko Haram suka yi garkuwa da su a hanyar Maiduguri – Damaturu, jihar Yobe.
Jami’an tsaron sun shiga can cikin dajin suna farautar wadannan mutane har suka kai ga wani kauyen da babu kowa sai su Boko Haram din da wadannan mutane da suka yi garkuwa da su.
Da Boko Haram suka hango mu mun tunkare su sai suka arce cikin kungurmin daji suka kyale mutanen a wannan kufayin gari.
Jagoran rundunar, Abioye Babalola ya shaida wa wakilin mu cewa Allah ya ba su nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su 13 a titin Maiduguri zuwa Damaturu.
” Da suka ga mun tunkaro su da yawan mu sai suka arce cikin daji suma kyale wadanda suka yi garkuwa da su a wannan kauye da yanzu babu kowa a cikin sa. Da ma kuma mun dade muna bin sawun su.
Yanzu sabon abinda suka tsiro da shi shine na yin garkuwa da mutane a babbar titin Maiduguri – Damaturu.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin sako daliban makarantar Kagara da mahara suka yi ranar Asabar bayan sun shafe kwanaki 10 tsare a cikin daji.
A jihar Zamfara ma, wasu ‘yan mata har sama da 300 na tsare a hannun’ yan bindiga da suka yi garkuwa da su ranar Juma’a a Jangebe, Karamar Hukumar Talatan Mafara.
Discussion about this post