Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sace daruruwan daliban Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Jangebe a jihar Zamfara a matsayin rashin hankali da mutunci cewa sam ba za a yarda da shi ba, sannan da isar da gargadi mai karfi ga ‘yan bindiga da masu daukar nauyinsu cewa su shiga taitayin su, tura yanzu ta kai bango.
Garkuwa da daliban Jangebe ya auku ne kimanin kwanaki 10 bayan sace dalibai, malamai da iyalan malamai har 42 a garin Kagara, jihar Neja. Suma suna cen tsare hannun ‘yan bindigan ba a san halin da suke ciki ba.
Shugaba Buhari ya kara da cewa ” Abinda da ya ke kawo wa dakarun Najeriya cikas wajen tunkarar wadannan ‘yan bindiga kai tsaye shine, don bin Ka’idojin yaki, ba za a iya afka wa inda mutane suke ba ko kuma inda suke zagaye da mutanen da suka yi garkuwa da su, idan da ba haka ba kuwa da an wuce wurin.
” Muna da karfin da za mu bi wadannan ‘yan bindiga duk inda suka mu fatattaka su, amma abinda ke sa dole mu bi a hankali shine irin rayukan da za a rasa na wadanda basu ji ba basu gani ba, wato mazauna kauyuka da kuma wadanda aka yi garkuwa da su. Za a rasa rayuka da dama. Wannan shine kawai yake sa mu dan yi jinkiri.
Buhari ya yi karin haske cewa dole sai an rika bi sanu-sannu a hankali idan har ana son a ceto wanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da. Domin kada a jefa shi cikin tashin hankalin da ya wuce wanda ya ke ciki da kuma kubutar da shi ba tare da sun illata shi ba.
” Kada ku dauka ja da baya da gwamnati ke yi don kare rayukan mutanen da kuka sace a matsayin tsoro ko kuma kun fi karfin gwamnati ne, a’a, ba haka bane
A karshe ya gargadi wasu gwamnonin da ke yin sulhu da ‘yan bindigan cewa, su yi taka-tsan-tsan da wannan shawara domin kada reshe ya juya da mujiya nan gaba.