Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa ya zuwa ranar 15 ga Fabrairu, hukumar ta karbi bukatun da ba ta nema ba har guda 9,777 daga sassan kasar nan na karin rumfunan zabe.
Shugaban Hukumar ne Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a ranar Talata.
Ya lura da cewa wadannan bukatu da aka kawo, wadanda guda 5,700 ne a Oktoba 2020, sun karu da sama da 4,000 a cikin watanni hudu kacal.
Yakubu ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci ofishin Kungiyar Tuntuba ta Mutanen Arewa (ACF) a Kaduna ranar Talata domin tattaunawa kan batun karin rumfunan zabe a kasar nan.
Shugaban hukumar ya ce dalilin ziyarar tasa shi ne domin ya gana da shugabannin kungiyar ta ACF saboda ya yi masu bayani kan tsarin da hukumar ta ke da shi na kara yawan rumfunan zabe a kasar nan.
Ya kara da cewa batun da ake yi na karancin rumfunan zabe babbar matsala ce da ta shafi kasa baki daya.
Ya ce: “Tun a cikin 1996 mu ke da rumfunan zabe guda 119,973, amma yawan su bai canza ba saboda tun a 1996 aka yi kiyasin cewa za su iya daukar masu zabe da aka yi wa rajista mutum miliyan 50.
”A cikin 1999, kasar nan ta na da masu zabe da aka yi wa rajista mutum miliyan 84 amma kuma yawan rumfunan zaben bai sauya ba.”
Ya yi nuni da cewa a dalilin haka, ana samun dimbin cinkoso kuma hakan ya na matukar kuntata wa masu zabe a ranar zabe.
Yakubu ya ce hukumar ta na so ta ja hankalin kowa da kowa don a inganta tsarin dimokuradiyya.
Ya bayyana cewa an fara bin hanyar da za a gyara lamarin tun a makon jiya lokacin da hukumar ta yi zaman tattaunawa da jam’iyyun siyasa, kungiyoyi, hukumomin tsaro da kuma kafafen yada labarai.
Ya kara da cewa tuntubar juna wani muhimmin abu ne a kowace dimokuradiyya, kuma hakan ne ya sa hukumar ta ga ya dace ta yi tuntuba, saboda ta samu ra’ayoyin ‘yan Nijeriya daga ko wane lungu da sako.
A cewar sa, hukumar ta na fadada tattaunawar da ta ke yi zuwa kungiyoyin zamantakewa da al’adu, da na gargajiya da na addini, da hukumomin gwamnati irin su Majalisar Tarayya da Cibiyar Zartaswa ta Tarayya (FEC) da Cibiyar Gudanar da Kasa.
Ya ce hukumar ta tuntubi dukkan kungiyoyi a sassan kasar nan kuma har wasu sun fara turo da sakonni ta hanyar tes.
A lokacin da ya ke maida jawabi, Sakatare-Janar na ACF, Alhaji Murtala Aliyu, wanda shi ne ya tarbi shugaban na INEC da tawagar sa, ya bayyana jin dadi da ziyarar, ya ce kungiyar za ta ci gaba da goyon bayan duk wani shiri da za a kawo da nufin inganta rayuwar jama’a da kuma kasar baki dayan ta.
Ya ce, “Tun a cikin 1996 ba a kara yawan rumfunan zabe ba. Mu na ganin ya dace a kara yawan su don a saukaka wa tsarin dimokuradiyya.”
A cewar sa, “Daya daga cikin matakan wucin gadi da aka dauka shi ne kirkirar wasu rumfunan zabe wadanda aka lika da manyan rumfuna, kuma hakan ya samu karbuwa a wurare da dama. Saboda haka abin da ake bukata shi ne a maida su rumfuna masu cin gashin kan su.”
Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya masu kishi
da su ilmantar da jama’a kan batun fadada rumfunan zabe saboda a tabbatar da dorewar su.