Hukumar tace fina-finai ta kama jibgin fina-finan batsa a Sokoto

0

Hukamar Tace Fina-finai ta Kasa (NFVCB), ta kama tulin fina-finan batsa da wasu fina-finan da ba a tace kafin a fitar da su ba, a Sokoto.

Jami’an hukumar tare da sauran jami’an tsaro ne su ka yi gangamin rangadin kamen fina-finan batsa a wurare daban-daban, da su ka hada da kan titin Ahmadu Bello Way, Emir Yahaya Way and Abdullahi Fodio Road duk a cikin Sokoto.

Babban Daraktan NFVCB, Adebayo Thomas, ya bayyana cewa ana kwace wadannan haramtattun kayayyaki ne a kasuwa, kuma za a kona su domin ya zama darasi ga sauran masu yin irin wannan mummunar sana’a.

Ya ce fayafayen bidiyon da aka kwace sun hada da DVDs, tulin CDs masu dauke da tulin fina-finai a cikin CD daya da sauran fina-finan da ba a tace ba, cikin kuwa har da tulin fina-finan batsa.

“Mun kai farmaki har wuraren da ake rikodin din wadannan fina-finai ana danna su cikin kasuwa. Kuma mun yi nasanar kwace na’urorin rikodin din fina-finan.

“Sannan kuma mun kai farmaki shagunan masu sayar da irin wadannan fina-finai, wadanda yawancin su kwafe-kwafe ne ake yi daga original, sai kuma wadanda ba su da lasisi ko ba a tace su ba.

“Irin mutanen da ke sayarwa ko safarar wadannan fina-finai, su na haddasa wa masu shirya fina-finai na ainihi asarar bilyoyin nairori. Dalili, saboda su ke shigo da fina-finan jabu wadanda ba original ba su na kuma yin rikodin sun a sayarwa. Maimakon a rika sayen wanda kafani ya fitar tun da farko.

“Sannan kuma wannan haramtacciyar kasuwa da su ke yi, ta na tauye wa gwamnati samun kudaden shiga.

Ya ce za a fadada wannan farmakin kamen fina-finan rikodin, na makauniyar kasuwa da na batsa a Kaduna, Abuja, Onitsha da Aba.

Ya kara da cewa tun da farko sun samu rahoton sirri ne cewa garin Sokoto ya zama wata cibiyar buga fina-finan wanki da haramtattun fina-finai da kuma fina-finan batsa a Arewa. Kuma da su ka kai farmaki a Sokoto din, sun tabbatar da hakan.

Thomas ya yi tsokacin cewa tilas hukumar sa ke tashi tsaye wajen kakkabe fina-finan batsa, domin sun a gurbata tarbiyya.

Share.

game da Author