Hukumar NCDC ta daina bayyana sakamakon Korona Kullum sai duk mako

0

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa daga yanzu hukumar ba za ta rika fidda sakamakon gwajin Korona kullum ba kamar yadda ta ke yi a baya ba, mako mako za ta rika fidda wa.

“Daga ranar Litini hukumar za ta daina saka sakamakon gwajin cutar a kulum a shafin ta na yanar gizo.

Duk da cewa yanzu babu sakamakon gwajin cutar da zai nuna yawan mutanen da suka kamu da cutar bincike ya nuna cewa Najeriya ta fara samun sauki wajen yaduwar cutar.

Binciken ya nuna Najeriya na samun karuwa a yawan mutanen dake warkewa daga Korona a kullun.

Yaduwar Korona

Zuwa yanzu mutum 139, 242 ne suka kamu da cutar sannan daga ciki an sallami mutum 112, 557.

Cutar ta yi ajalin mutum 1, 647 a jihohi 36 a kasar nan.

Jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –51,685, FCT–17,824, Filato –8,297, Kaduna–7,818, Oyo–5,905, Rivers–5,759, Edo–4,006, Ogun–3,578, Kano–3,314, Delta–2,396, Ondo–2,506, Katsina–1,901, Enugu–1,829, Kwara–2,158, Gombe–1,802, Nasarawa–1,976, Ebonyi–1,540, Osun–1,805, Abia–1,338, Bauchi–1,164, Borno-1,085, Imo–1,220, Sokoto – 759, Benue- 917, Akwa Ibom–1,090, Bayelsa 695, Niger–847, Adamawa–673, Anambra–1,271, Ekiti–641, Jigawa 485, Taraba 496, Kebbi 276, Yobe-250, Cross River–222, Zamfara 215, Kogi–5.

Jihar Legas ita ce jihar da yaduwar cutar ta fi yi wa tsanani a kasar nan.

Sauran jihohin da yaduwar cutar ta yi tsanani a cikin su sun hada da Abuja, Kaduna, Filato da Oyo.

Share.

game da Author