Hukumar NALDA za ta horas da manoma 21,000 a jihar Adamawa

0

Shirin inganta aiyukkan noma da samar da abinci na hukumar inganta aiyukkan noma da filaye na ƙasa NALDA dake jihar Adamawa za ta horas da manoma 21,000 a jihar.

Kodinatan NALDA Zachariya Kraha ya sanar da haka ranar Laraba a garin Yola.

Ya ce Shirin zai horas da akalla manoma 1,000 a kowace karamar hukumar jihar.

“Bayan an kammala horas da manoman shirin zai dibar wa kowani manomi fili sannan za a bashi taki, maganin feshi da sauran kayan aiki noma domin su fantsama aiki.

“Bayan an yi girbi kuma, sai gwamnati ta siya amfanin gonan da suka noma ba tare da sun wahala ba.

“Yin haka zai taimaka wajen samar da aiki yi sannan da kawar da matsalar yunwa da karancin abinci a jihar da kasa baki faya.

Bayan haka Kraha ya ce a karkashin shirin za a kuma horas da wadanda suka yi karatun digiri 83 dabarun aikin manoma na zamani.

Ya ce a yanzu haka manoman rani 1,500 a jihar sun yi rajistan samun horo Kan noman shinkafar rani.

Kraha ya yi kira ga wadanda gwamnati za ta horas ka karkashin wannan shiri da su mai da hankali wajen sanin abinda za a rika koyar da su a lokacin wannan tirenin.

Fannin gona na daga cikin fannonin da gwamnatin Najeriya karkashin Shugaba Muhammadu Buharita fi maida hankali a kai.

Share.

game da Author