Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba ta cire Najeriya daga cikin jerin Kasashen da za su samu allurar rigakafin Covid-19 ba – Bincike DUBAWA

0

Jam’iyyar PDP a Najeriya ta bayyana a wani rahoto na ta cewa Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) ta cire Najeriya daga cikin jerin Kasashen duniya da za su samu allurar rigakafin Korona, (Covid-19).

Cibiyar gudanar da bincike ta DUBAWA ta bi diddigin wannan magana domin bankado ainihin gaskiya da sahihancin wannan korafi na jam’iayyar PDP a Najeriya.

Zargi: PDP na zargin cewa WHO ta hana Najeriya allurar rigakafin COVID-19

Labarin da jam’iyyar PDP ta bayar cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta hana Najeriya allurar rigakafin COVID-19 bisa rashin cancanta ba gaskiya ba ne. Jami’an WHO sun karyata labarin

Annobar sabuwar cutar COVID-19 ta zo da sabbin matsalolin da hatta kasashen da suka cigaba sai da suka shiga wani hali na ha’ula’i. Daga farkon zuwan cutar, ko kwararru wajen binciken asalin kwayoyin cuta sai da suka dauki lokaci suna bincike kafin suka gano bakin zaren. Sai dai duk da haka, an sami cigaba sosai wajen gano hanyoyin takaita yaduwar cutar da ma samar da rigafin da zai iya kare mutane daga kamuwa da ita.

A ‘yan watannin da suka gabata, wannan cigabar musamman yadda ta shafi kirkiro alluran rigakafin COVID-19 ta janyo cece-kuce da rahotanni mabanbanta dangane da yadda kasashe za su sami allurar. A watan Janairun shekara ta 2021, gwamna Kayode Fayemi shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya ce:

“Najeriya na cikin kasashen Afirka goma sha biyun cikin kasashe 92 da aka tantance a matsayin wadanda suka cika sharuddan samun allurar rigakafin. Dan haka za ta sami kason farko a karshen watan Fabrairu.”

To sai dai ba da dadewa ba aka sami bayanan da ke karyata furucin Mr. Fayemi. A shafin Twitter, jam’iyyar adawa ta PDP wadda ta kasance kwakwarar adawa ga jam’iyyar APC mai mulki ta yi zargin cewa hukumar WHO ta cire Najeriya daga jerin kasashen da suka cancanci samun allurar rigakafin. Masu zargin sun ce hukumar ta dauki wannan matakin ne domin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta gaza samar da irin wuraren da ake bukata dan ajiye ruwan alluran.

PDP ta wallafa zarginta a shafin twitter tare da wata sanarwa kamar haka:

Fabrairu 6 2021

Sanarwa ga manema labarai

Allurar rigakafin COVID-19: Jam’iyyar PDP ta baiwa Buhari laifi bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Najeriya ba ta cancanci samun allurar rigakafin ba.

PDP ta ce hukumar WHO ta cire Najeriya daga jerin kasashen da suka cancanci karbar allurar rigakafin COVID-19, sakamakon gazawar gwamnatin Buhari wajen samar da wuraren ajiye magungunan wanda hakan ya tabbatar da matsayinta na cewa gwamnatin APC ta gaza.

Jam’iyyar ta ce abin kunya ne wanda kuma bai kamata a yafe ba, a ce kasa mai mahimmanci kamar Najeriya ta rasa allurar rigakafin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta taimaka a samar. Gazawa da cin hanci da rashawa sun taru sun hana gwamnatin APC samar da wurin ajiyar da ke da sanyin digiri 70 kasa da sifili a bisa ma’aunin selshiyos. Wannan kuma duk da yawan billiyoyin Nerar da ta ce ta kasha wajin yaki da cutar ta COVID-19.

Lallai wannan abun kunya ya sake karfafa matsayarmu na cewa gwamnatin APC ba za ta iya gudanar da gwamnati ba, kuma don haka ne kasarmu ke fama da matsalolin tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

A watan da ya gabata jam’iyyar mu ta gargadi gwamnatin Buhari dangane da matakai marasa gamsarwar da ta dauka wajen samun allurar rigakafin da ma sauran abubuwan da suka danganci cutar. Sai dai ta sa kafa ta shure gargadin da duk shawarwarin da muka bayar.

Yanzu ‘yan Najeriya sun shaida da idonsu cewa duk wani ikirarin da ta yi na bayar da kai, ya tsaya a sanarwar da ta yi a kafofin yada labarai. Babu abun da take yi da ya wuce sanar da adadin mutanen da suka kamu da cutar, wadanda suka warke da wadanda suka riga mu gidan gaskiya. Babu matakin da ta dauka wajen binciken cutar, mafarinta da yadda ta ka iya sauyawa ko kuma idan Najeriya na da wani nau’in cutar da ya banbanta da na saura. Sannan ba ta samar da kayayyakin aiki ba, da ma wajen ajiye allurar rigakafin domin kasar ta kaucewa cutar baki daya.

Bugu da kari, wannan ya sake tabbatar da matsayarmu na cewa mambobin kwamitin da shugaban kasa ya baiwa nauyin kula da lamuran da suka shafi cutar wato Presidential Task Force (PTF) ba su cancanta ba. ‘Yan siyasa ne kawai wadanda basu da masaniyar da ake bukata na shawo kan wannan annobar a kasarmu. Ya kuma halatta kiraye-kirayen da ake yi na rusa wannan kwamiti na PTF

Abun takaici ne a ce saboda gazawa da cin hanci da rashawar gwamnatin APC, kasarmu, wadda ta taba kasancewa jagora a matakin kasa da kasa tana kuma gogayya a fannoni daban-daban, yau an wayi gari ta durkushe, hatta abu kankani kamar allurar rigakafi ya gagareta.

Sakamakon wannan lamari mai muni ne muke sabonta kirarmu na rusa kwamitin PTF cikin gaggawa a baiwa ‘yan kasuwa masu zaman kansu damar daukan matakan da suka dace tunda gwamnatin Buhari ta gaza.

Jam’iyyarmu na kira ga duk masu kishin kasarmu da jami’an kiwon lafiya da masu sarrafa magunguna da masu kula da aikin sufuri da su hada kai su taimaka wajen ceto Najeriya daga halin da ta shiga.

Haka nan kuma, PDP tana baiwa shugaba Buhari shawara da ya amince da gazawar gwamnatinsa ya nemi taimako daga kafofin da suka dace sannan ya kwafi matakan da jam’iyyar PDP ta yi amfani da su wajen shawo kan cutar Ebola a matsayin matakin da aka tabbatar zai yi aiki wajen kawar da cutar COVID-19

Sa hannu:

Kola Ologbondiyan, Sakataren Jam’iyya ta kasa

Sanarwar PDP ta dogara da hujja guda daya ne, na cewa WHO ta hana Najeriya allurar domin gwamnati ta gaza samar da wurin ajiya. Dan haka ne wani mai amfani da shafin twitter mai suna Yusuf Yunusa (@yyunusa) ya yi wata tambaya mai cewa:

“Wane ne ke yada wannan labaran karya?”

Dubawa ta binciki kafafe da dama dan tantance ko wannan batu na allurar rigakafin na da gaskiya ko karya ce. Abun da ya sa yin hakan ke da mahimmanci shi ne irin wannan labari zai iya jan hankalin mutane da yawa idan kuma ya kasance karya an yaudari jama’a ke nan. Shi ya sa Dubawa ta dauki nauyin tantance gaskiyar maganar.

Tantancewa

Dubawa ta ji ta bakin Kate Ribet, jami’ar sadarwa a sashin kula da samar da allurar rigakafi na ofishin WHO da ke yankin Afirka sannan ta tambayeta ko Najeriya da gaske ba ta cancanta ba, jami’ar ta ce WHO ba ta hana kowa samun allurar rigakafi a Afirka ba daga COVAX, wadda ita ce hadakar kasa da kasar da za ta tabbatar kasashen duniya sun sami allurar yadda ya kamata.

Bugu ta kari, hukumar WHO na yin iya kokarinta ne ta ga cewa kowa ya sami allurar a kan lokaci.

A yanzu haka ana sa ran duk kasashen Afirkan da suka cancanta, za su fara samun allurar AstraZeneca/Oxford daga karshen watan Fabrairu. Daya daga cikin abubuwan da ke janyo jinkiri shi ne binciken da WHO ke gudanarwa dan ganin ko za a iya amfani da allurar cikin yanayi na gaggawa, kuma nan ba da dadewa ba za’a sami sakamakon wannan binciken.

Daga cikin allurai milliyan 88 da aka baiwa Afirka a matakin farko, kason Najeriya ya fi na kowa yawa domin ta sami milliyan 16.

Ribet ta kuma yi Karin bayani:

“Baya ga kason Astra Zeneca akwai kuma na Pfizer wadanda duk za a iya samu ta COVAX. Da farko Pfizer ta bayar da milliyan daya da dubu dari biyu amma bai kai ko’ina ba. Kasashe 72 suka fara mika bukatarsu ga COVAX kuma kwamitin tantancewa ta amince da 51 (Najeriya ta kasance cikin wadannan kasashe) Daga baya an amince da wasu kasashe 18 su karbi kason Pfizer. A nahiyar Afirka, daga 18 ga watan Janairu, kasashe 13 suka nuna sha’awar samun allurar, daga ciki an amince a fara da guda tara kuma Najeriya ta kasance a cikinsu.”
Dangane da tangardar da aka samu wajen kawo allurar Najeriya ta yi karin haske:

“Mun sami karancin alluran Pfizer saboda haka ba duka kasashe 51 da aka tantance suka samu ba saboda wasu matsaloli. Misali Pfizer ba za ta iya hada kasashe da dama a lokaci daya ba. Dan haka idan aka ce kowacce a cikin kasashe 51 sai sun samu, ba za a cimma abin da ake so ba. Dan haka ta fara mayar da hankali kan kasashen da ke biya daga aljihunsu, sannan aka yanke shawarar daidaita samar da allurar tsakanin masu saye da kudinsu da wadanda ke samu daga yankuna shidda (6) na hukumar WHO.”

Lallai martaninta ya nuna cewa WHO ba ta hana Najeriya samun allurar rigakafin COVID-19 ba. A yanzu haka ma tana jiran zuwan kasonta ne.

Daga Karshe

Sanarwar jam’iyyar PDP cewa WHO ta cire sunan Najeriya daga jerin kasashen da suka cancanci samun allurar rigakafin COVID-19 ba gaskiya ba ne. Jami’ar da ke kula da sadarwa a hukumar WHO ta tabbatar cewa hakan karya ne.

Share.

game da Author