Cikin shekarar 2004 Chinoso Asonyo wata akawu ce ta wani kamanin harkar mai a Lagos. A lokacin da auren ta da yara hudu.
Sai dai kuma rayuwar ta a takure ta ke, kamar sauran mazauna Legas, kasancewa ta na tun da jijjifin asubahi ta bar gida zuwa wurin aiki, sai karfe 11 na are ta ke komawa gida.
Haha Chino ta kasance cikinn wannan hakilon rayuwa, in banda ranar kowace Lahadi kadai.
Da ya ke mijin ta soja ne, ya kasance ana yawan yi masa canjin wurin aiki. Don haka sai ta nemi samun wata sana’ar da za ta rika yi domin ta samu zama wuri daya tare da yaran ta su hudu.
Ranar wata Asabar ta isa ofis, bayan sa’a biyu sai mijin ta ya dira ois din ya ce ya na bukatar a bai wa matar ta sa takardar sallama daga aiki. Wato ta ajiye aiki kawai nan take.
Ya yi wannan bukatar ne saboda ya na bukatar matar ta sa ta rika zama ta na kula da yaran su.
“Yana fadar haka, sai na fahimce shi, kuma ban ga laifin sa ba. Nan da nan na rubuta takardar ajiye aiki.’’
Haka Chinaso na tafi wajen wata kawar ta rai a bace, ta fara koya mata sana’ar kiwon kifi.
Bayan shekara 17 a yanzu Chinaso ta na cikin shukura da hamdala saboda ta ba ganin ba ta yi saki-na-dafe-ba.
A yau da gobe ita ce Shugabar Katafariyar Gonar Chielo Farms, Lagos.
Ta fara da kiwon kifaye 2000 da jarin naira 800,000. Amma a yanzu ta na da kifaye sun kai 120,000.
Baya ga katafariyar gonar kiwon kifin ta, Chinaso ta na da babbar gonar kiwon kaji, kuma ta na noman shinkafa, rogo, kayan miya sannan kuma ta na cashe shinkafa.
Kafin bullar cutar korona, har kasar Amurka Chinaso ke loda kifi ta na turawa ana sayar mata.
Ta taba cin lambar gwarzuwar kiwon kifi ta jihar Lagos a cikin 2014.
Daga nan ne ta kafa Kungiyar Mata Masu Kiwon Kifi ta Jihar Lagos.
Wannan matar ta na daga cikin sahun farko na wadanda su ka fara cin gajiyar Shirin Rice for Job’, wadda a cikin manoma 30, su takwas ne su ka ci gajiyar shirin har karshe.
Daga nan ne ta fara noman shinkafa na hekta biyar a yankin Ijebu, Lagos.
Ta sha gaganiya kafin ta ci ribar noma sosai, amma sannu a hankali ta daure, har ta yi gamo-da-katar.