HIMMA DAI MATA MANOMA: Yadda ‘yan bindiga su ka raba ni da gona, na koma sayar da garin citta da sana’ar zuma – Mirza

0

Asma Mirza mace ce mai himma da kokarin noma matuka, a Jihar Kaduna. Amma duk da wannan kokari na ta, sai da rashin tsaro ya yi tsanani har ta kai saboda gudun kada ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane su sace ta, sai ta hakura da noman tun a cikin 2018.

Amma kafin Mirza ta hakura da noma, ta kasance mai nasibi sosai a harkar noma, musamman irin yadda ta ke hada-hadar noma irin shinkafa na zamani mai inganci, wanda Gwamnatin Tarayya da Ma’aikatar Gona da Cibiyoyin Bunkasa Noma da Binciken Dabarun Aikin Gona kan kwadaitar a rika nomawa. Wato Rice Hybrid Seeds.

Shi Asma Mirza ta rika shukawa, idan ta girbe sai ta rika sayar wa masu noman kasuwanci, har ma da masu noman shinkafar da za su ci a gida kawai.

“Amma yanzu gona ta gagare mu zuwa, kai ko ziyara ma ba na iya zuwa. Mutanen karkara da ke makwautaka da gonakin su a inda na ke noma a baya, sun shaida min ai su ma zuwa gonakin su ya gagara.

“Duk wanda ya kuskura ya je gona, to shi ya janyo wa kan sa. Saboda ba ka ankara ba sai masu garkuwa su damke ka kawai.

“Amma fa ana samun daidaikun mutane masu kasada da kuma saida rai. Su kan je gona, sai dai su din ma, idan sun je ba tsayawa su ke yi su aiki tukuru a gonakin su ba.

“Zuwa gonar su ke yi kamar mai dibar wuta da hannu. Wuf, har ka shiga ka fito, ka dawo gida.Cikin kankanen lokaci kamar fitar harsashen bindiga ake zuwa gonar, a yi sauri a koma gida.”

Mirza ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa da ta ga zaman-dirshan a gida ba zai yi mata ba, tunda ta daina harkar noman hekta 30 da ta ke yi, sai ta yi dogon tunani, ta yi zanari, kuma ta gano cewa a yanzu mata masu yin abinci kowace sauki ta ke nema.

Mirza sai ta fara yin sana’ar daka ganyen miyar okro, ta nika shi ta maida shi gari, ta na sayarwa. Daga nan da ta ga abin akwai nasibi, sai ta hada da nika garin citta ta na sayarwa.

“Ana bukatar garin citta sosai, domin ana zubawa a abinci, a lemon sha, ana zubawa a ruwan shayi da sauran nau’ukan abinci daban-daban. Citta na kara dandano da dadin abinci sosai. Ita kanta cittar ana yin shayin ta.

Bayan wadannan kuma na hada da sana’ar zuma, wadda ita ma akwai nasibi a cikin kwarai da gaske.

Mirza ta ce ta maida himma sosai wajen yin wannan sana’a, musamman lokacin kullen korona, wanda aka tilasta wa kowa zama gida.

Sai dai kuma duk da haka, ta ce ba za ta manta da harkar noma ba. Yanzu haka ma fata da addu’a ta ke yi komai ya lafa, a samu zaman lafiya, ta ci gaba da harkokin noman ta.

Harkar citta da zuma da garin okro kuwa, Mirza ta ce sana’ar ita ma ta karbe ta, ba ta ma san wadda ta fi nasibi ba, tsakanin noman da harkar garin citta, okro da sana’ar zuwa.

Dalili kenan ta ce ita ko da ta koma harkokin noman ta, to ba za ta iya barin wannan sana’ar ba. Domin baya ga citta da okro, ta na kuma harkar nika da sarrafa wasu nau’o’in kayan miya za su kai sinadarai biyar.

Share.

game da Author