HIMMA DAI MATA MANOMA: Ban taba samun tallafin noma daga gwamnati ba, duk da kusanci na da Abuja – Mero mai noman shinkafa

0

Shekarun Meru Musa 35, kuma ta na da ’ya’ya shida, ta shaida wa wakillin mu yadda ta tsinci kan ta cikin harkokin noma ka’in-da-na-in.

“Tun ba a dade da yi min aure ba, miji na ya shiga matsalar da ciyar da iyali ma na neman gagarar sa. Ta kai ga sai mun jira ya je gona a kullum ya debo kayan abincin da za mu ci. Ko kuma ya fita fagamniyar nemo kudin da za mu sayi abinci.

“Mu na zaune a wani kauye da ake kira Kutara. Noma ne sana’ar mutanen kauyen. Saboda haka babu wani abin da mutum zai yi ya tsere wa fatara, yunwa da talauci sai fa noman nan. To sai na ga gara kawai ni ma na fada harkar noman na taimake shi.

“Iyaye na manoma ne. Ba su saka mu cikin makarantar zamani ba. Ilmin da kawai su ka koya mana, shi ne noma.

“A yanzu haka da na ke magana, gona ta ba babba ba ce. Girman ta bai wuce hekta daya ba, amma ina kokarin kara samun wata gonar.

“Kuma wannan noman ya na tattare da matsaloli. Samun takin zamani ma wata babbar matsala ce. Wasu lokutan fag a ka da kudin takin zamani a hannu, amma ka neme shi a kasuwa ka rasa.

“Saboda haka sau da yawa na kan yi amfani da kashin shanu da kuma rubabben abinci a matsayin takin shinkafar da na ke nomawa.”

Mero wadda ba ta fi shekaru biyar da fara noma ba, ta shaida wa wakilin mu cewa a kasuwa ta kan sayo irin shinkafar da ta ke shukawa. Amma wani lokacin ta kan rage irin shinkafa daga cikin wadda ta noma, domin sake shukawa a kakar noma ta gaba.

Ta kara da cewa ta fi son noman shinkafa, saboda ya karbe ta, kuma kasar da ke yankin su ta fi son shinkafa sosai.

“Sannan kuma ka ga baya ga wadda na ke tanada ina sayarwa, ita wannan shinkafar ni da iyali na mu ke ci.”

Da aka tambaye ta ko ta na samun irin shinkafa na zamani da gwamnati ke bayarwa ga manoma? Sai Meru ta ce, “Ina dai jin labarin sa kawai. Idan ina tafiya zuwa Gwagwalada, akwai wani ofishin Hukumar Irin Shuka da na taba jin cewa wai su na bayarwa. Amma ni dai ba a taba ba ni tallafin komai ba. Duk kuwa da kusancin da na ke da shi da Abuja, Babban Birnin Tarayya.

Sannan kuma ta ce ba ta taba amfani da injinan noma na zamani ba, domin ba ta iya sayen su ko daukar su haya.

“Amma a cikin yara na akwai guda biyu wadanda sun dan tasa. To idan su ka taso daga makaranta, ko kuma a lokacin hutu, su na taya ni noma.”

Ta ce ta kan samu buhu 8 zuwa 10 na babban buhu mai nauyin kilogiram 100.

Batun adana kayan abinci kuwa, sai Meru ta ce ba ta da wurin ajiya, amma haka nan ta kan kukuta a cikin dakin su ta ajiye shinkafar a wurin da su ke kwanciya a kuntace.

Ta ce ba ta cika kai shinkafa kasuwa ba, domin akwai masu zuwa har cikin gona su na saye idan ta kosa.

Amma idan lokacin da ba su kai ga zuwa ba, ko kuma su ka je su ka sayi wadda ta wadace su, to ta kan kai kasuwa mafi kusa da ita.

Ta ce mijin ta na taya ta noma tabbas. Amma a bangaren kungiyoyin mata manoma, ta ce ba ta kai kan ta ciki saboda da wahala ka ga irin wadannan kungiyoyin na cin moriya ko amfanar kungiyoyin bata tallafi na NGOs ko gwamnati, sai dai wahala kawai.

Babban kalubalen ta ga noma a matsayin ta na mace, bai wuce matsalar karancin jari ba, sai kuma rashin wadatacciyar gona ko gonakin nomawa.

Share.

game da Author