Kungiyar Kare Hakkin Jama’a mai suna HEDA, ta aika wa Shugaba Muhammadu Buhari wasikar tunin sanar da shi cewa akwai wasu shari’u da binciken sata da harkallar kudade guda 25 manya-manya, wadanda shekaru da dama an ma daina tayar da maganar su.
HEDA ta shaida wa Buhari a cikin wasikar cewa wadannan harkalloli da aka dade ba a ma tayar da zancen su, akwai alamomi na cewa an binne su karkashin tabarma an zauna a kan su.
Idan haka ne kuwa, sai kungiyar ta ce to an karkatar wa Najeriya makudan kudaden da su ka kai har naira bilyan 900.
Shari’un kamar yadda HEDA ta bayyana a jadawalin sunayen su, sun kai na harkallar kudaden da su ka kai naira bilyan 900.
Wasikar dai an aika ta Fadar Shugaban Kasa a cikin wannan makon, tare da yin karin bayani a cikin ta cewa Najeriya sai kara dulmiyawa cikin dagwalon kazantar cin hanci da rashawa da satar kudaden gwamnati ta ke ta yi gadan-gadan.
Sannan kuma HEDA ta kara da cewa mutane masu kashi a gindi ne kan gaba wajen hayewa shugabancin wasu hukumomin da ke hana ruwa gudu a yaki da cin hanci da rashawa yanzu a kasar nan.
Cikin wasikar, Shugaban HEDA Suraju Olarewaju, ya bayyana wa Buhari cewa harkallolin satar kudaden da aka zaune su akan tabarma, ko ana binne su a kasa sun kai na naira bilyan 900 daga shekarar 2015.
Wasikar ta ce wadanda ta lissafa din su 25 ba su kenan ba, akwai ma wasu kanana masu yawan gaske, wadanda an danne, an binne ko kuma an manta da ci gaba da su.
Akwai badakar Shugaban Bankin Fidelity Bank, Nnamdi Okonkwo, wanda EFCC ta kama cikin 2015 ta kudi dala milyan $115 wadanda ya karba daga hannun Tsohuwar Ministar Fetur, Diezani Alison-Madueke; sai badakalar Darakta a First Bank Plc, Dauda Lawal, wanda EFCC ta gurfanar bisa laifin karbar dala $25 daga cikin da milyan $153m da Alison-Madueke ta yi wa rabon goron daurin aure.
Sannan akwai badakalar marigayi Dikko Inde Abdullahi Dikko, wanda aka zarga da wawure naira bilyan 40, amma kotu ta ce ya maida naira bilyan 1.4 kacal.
Sannan kuma HEDA ta ci gaba da lissafa wa Buhari wasu badakala da dama, ciki har da wadanda ta ce wasu manyan jami’an gwamnatin Buhari su ka bada umarnin a daina binciken su.
Misalin irin wadannan sun hada da badakalar makudan kudade NISRAL, wadda HEDA ta ce wasika ce aka aika wa EFCC da ICPC da DSS da NFIU cewa su daina wannan binciken badakalar wawurar kudade.
Akwai kuma kokarin da wasu jami’an gwamnati su ka yin a maida Abdulrasheed Maina kan mukamin sa.
Sai kuma yadda kiri-kiri Ministan Shari’a Abubakar Malami ya watsar da shari’ar Sanata Danjuma Goje ta zargin wawure naira bilyan 25 a cikin kwandon shara, ba tare da wata gamsasshiyar hujja ba.
Sai kuma zargin Laftanar Janar Tukur Buratai mai Ritaya ya sayi maka-makan kadarori a Dubai, duk HEDA ta ce wadannan da aka binne sun maida shirin yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin Buhari wata tatsuniya kawai.
Kungiyar ta ce wadannan shari’u da bincike duk su na kan tafin hannun ‘yan Najeriya da kasashen duniya.
Saboda haka kauda kai a kan su, tamkar kauda kai daga daraja da kima ce gwamnati ke wa kan ta.