HARE-HAREN ‘YAN BINGIDA: Kawunan gwamnanonin Arewa Maso Yamma a rarrabe yake – El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna ya bayyana cewa muddun ba a samu hadin kai tsakanin gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma ba, ba za a kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga ba.

El-Rufai ya kara da cewa bashi da ra’ayin ayi sulhu da ‘yan bindiga, amma wasu gwamnonin yankin basu son haka ba. Suna ganin yin sulhu da ‘yan bindigan zai kawo karshen hare-haren.

” Ni ban dalilin yin sulhu da dan bindiga ba, mutumin da ya saba ya na zaune a kawo masa miliyoyin naira a inda yake lokacin da yake so, ba zai yarda ko kuma ya hakura wai ya koma cikin halin da yake a baya ba sai yaga uwar bari.

” Abinda ya kama ta mu yi shine mu hada kai dukkan mu mu garzaya Abuja a bamu sojoji da zakakuman jami’an tsaro gaba daya a tura su cikin dazukan nan su yi wa mutanen nan farad daya. Shine maganin wannan matsala da ya addabe mu ba yin sulhu da dan ta’adda ba.

” Mun zauna da gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma, mun tattauna game da yadda ya kamata a tunkari wannan matsala amma kuma wasu daga cikin mu sun kafe da si dole a yi sulhu ne da ‘yan ta’adda maimakon a kawo karshen su kawai. Haka muka tashi taron da mukayi a Katsina.

A karshe El-Rufai ya ce yana tattaunawa da gwamnan Neja, Abubakar Sani wanda ra’ayinsu yazu daya lokaci-lokaci domin a kawo su yi nasu kokarin wajen dakile hare-haren da ake kaiwa a jihohin su musamman a iyakokin jihohin.

Share.

game da Author