Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa idan aka kammala gyaran katafaren Dandalin Bunkasa Al’adu na Na Kasa, wato National Arts Theatre da ke Lagos, za a samar wa akalla mutum 25,000 aikin yi a wurin.
Emefiele ya bayyana haka a Lagos, ranar Lahadi, wurin kwarya-kwaryar bikin sa hannun aikin sake farfado da Dandalin Bunkasa Al’adu a Iganmu, Lagos a ranar Lahadi.
Kashin farko na gyaran da za a yi wa Dandalin, zai kunshi kammala gina bangaren kade-kade da raye-raye, bangaren kayan kwalisa da ado, bangaren yada labarai da sadarwar zamani da kuma bangaren silima da kallon finafinai.
Dukkan wadannan bangarori an ce za a kammala su cikin watanni 15 kacal.
Emefiele ya ce ana fara wannan aiki za a ga “an samar wa matasa gagarimin ayyukan yi ka’in-da-na’in.
“Mun yi kintacen cewa za a iya samar wa mutum 10,000 kaitsaye aikin yi a lokacin aikin ginin dandalin a Cibiyar Samar Da Nishadntarwa ta Lagos.
“Sannan kuma mun yi kintacen cewa idan aka kammala aikin, akalla wasu mutum 25,000 za su samu ayyukan yi a dandalin. Sannan kuma wuraren samun ayyukan za su kara rubanyawa.” Inji shi.
Daga nan ya ce za a kashe naira bilyan 21.3 wajen kammala wannan bangare na farko na aikin gyaran dandalin.
An dai damka wa CBN wannan aikin gyaran dandalin ne, wanda tun a ranar Lahadi aka yi bikin sa hannun damka wa CBN aikin.