Gwamnatin Tarayya ta raba kayan noma ga kananan manoma masuyawa a Jihar Gombe.
Karamin Ministan Harkokin Noma da Raya Karkara, Mustapha Shehuri ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ma’aikatar sa ta fitar a ranar Lahadi.
Nanono ya ce akalla kashi 35 bisa 100 na wadanda za su amana da kayan noman, duk mata ne.
Wata sanarwa da kakain yada labarai ta Ma’aikatar Noma, Ezeaja Ikemefuna ya fitar, an ruwaito Karamain Ministan Gona Mustapha Shehuri na cewa hakan da aka yi zai kara bunkasa samar da abinci mai gina jiki, samar da aikin yi ga dimbin matasa da kuma bunkasa noman rani.
Minista Shehuri, wanda shi ne ya jagoranci raba kayan noman a Gombe, ya bayyana cewa kayan da aka raba wa kananan manoma, wani tallafi ne da gwamnati ta yi wa manoma domin rage masu radadin kuncin da su ka fada saboda kullen korona da kuma ambaliyar da ruwa ya yi masu a cikin daminar da ta gabata.
Ya ce ma’aikatar sa za ta ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga masana’antun da ke samar da kayan irin noma na zamani wadanda ke samar da abinci mai gina jiki da kuma kara habbaka harkokin noma a kasar nan.
Kayan Noman Da Aka Raba A Gombe:
An raba famfon ban-ruwa mai karfin Doki 3, wato 3HP guda 350, sai kuma mai karin 7HP guda 30, inji nan casa, injin feshi 70 da sauran kayayyakin inganta noma masu yawa.
“An kuma bayar da irin tumatir, tattasai da barkona, gwanda da sauran nau’o’i na kayan marmari da kayan gona a kananan hukumomi biyar na Jihar Gombe da kua kayan bunkasa noman rani domin samar da abinci mai gina jiki.”
“Kananan manoman jihar Gombe za su samu irin karo 10,000 kyauta, irin shinkafa metric tan 15 kyauta, metirik tan na irin gyada kyauta, da irin kashiw metirik tan 1,500 shi ma kyauta.” Inji Minista Sheriku.
”Wannan ma’aikata kuma ta yi irin wannan namijin kokarin a jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Kogi, Oyo, Cross River da Imo.”
Discussion about this post