Gwamnatin Kano ta kama jabun kwayoyi da kuɗin su ya kai naira miliyan 150 a Kano

0

Hukumar hana safara da saida muggan kwayoyi ta haɗa har Kano ta kama jabun kwayoyi da kudin su ya kai naira miliyan 150 a faɗin ƙasar har.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Kofar-Na’isa ya sanar da haka a wannan mako a garin Kano.

Kofar-Na’isa ya ce shugaban hukumar, Baffa Dan’agundi ya ja zugar zaratan ma’aikatan hukumar wajen yin aikin shaga shagunan saida magani ɗaya bayan ɗaya a karamar hukumar Ungogo.

“An yi wannan kame ranar 25 ga Fabrairu da karfe biyu na ranar.

“Dan’agundi ya yi kira ga mutane da kada su kasakasa wajen fallasa masu saida jabun magani a jihar. Hakazalika ya kara da cewa har kyauta za baiwa wanda ya tona asirin wadanda ke saida jabun magunguna a jihar.

Share.

game da Author