Kwamitin Sayar da Kadarorin da Aka Kwato Daga Hannun Barayin Gwamnati ya bayyana cewa zai kirkiro wata manhaja, wadda za ta kasance wani rumbu da a a rika tattara adadi, bayanai da darajar kadarorin da ake kwatowa.
Shugaban Kwamitin Dayo Akpata ne ya bayyana haka a ranar Talata, a lokacin wata ziyara da su ka kai ofishin EFCC a Abuja.
Akpata wanda Babban Sakatare ne a Ma’aikatar Shari’a, ya ce “kwamitin zai kafa manhajar rumbun tattara bayanan kadarorin da gwamnatin tarayya ta kwace, domin tattabar da cewa gwamnatin tarayya din ta samu kudaden da su ka kai darajar kadarorin da ta kwace.”
“ Za a fitar da tsari na bai-daya wajen sayar da kadarorin domin a guje wa yin asarar kadarorin. Idan mu ka yi haka, to gwamnati za ta amane su a cikin darajar su.”
Haka wata sanarwa da EFCC ta fitar ta ce Akpata ya fada a ziyarar da ya kai hedikwatar hukumar.
Daga nan ya jinjina wa irin aiki taren da hukumomin da abin ya shafa ke yi wadanda ke cikin kwamitin sayar da kadarorin.
“ Wannan ne karo na arko a Najeriya da hukumomi daban-daban su ka hadu wuri daya, a kan teburi daya su ka gudanar da aiki iri daya, wanda ya danganci kula da kadarori da kuma sayar da su.” Inji Akpata.
“ Saboda haka abu ne mai kyau da na kawo maku wannan ziyara domin tattauna yadda a mu yi aiki tare.”
A nasa bangaren Shugaban Rikon EFCC, Mohammed Abba, ya bayyana cewa hukumar za ta taimaka wajen yin aiki da kuma taya kwamitin aiwatar da nauyin da aka dora masa.
Sannan kuma ya yi alkawarin hada yadda kwamitin ai kai ziyara a dukkan shiyyoyin EFCC na kasar nan domin gane wa idon sa yawan kadarorin da hukumar da kwato da kuma wuraren da su ke.
An dai dora wa kwamitin nauyin sayar da dukkan kadarorin da aka kwato daga hannun barayin gwamnati a cikin watanni shida.