Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi karin haske game dsa kalaman da yayi a wajen taron Kungiyar ƴan jarida a Bauchi.
Gwamna Bala ya yi wannan karin bayani ne ta hannu babban mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Giɗaɗo.
Gwamnan ya ce bai dace ba ace wai an jingina ta’addanci da kashe-kashe ga wata kabila gaba ɗayanta ita kaɗai. Kowacce Ƙabila ta na da irin nata masj aikata barna da na kirki wanda irin sune ake fama da su a ko-ina a faɗin kasar nan.
” Dalilin haka ne gwamna Bala ya bayyana cewa irin waɗannan masu kiwon su ba tare da sun karya wata doka ba a matsayin su na ƴan kasa suke rike makami don kare kan su da dukiyoyin su daga barayin shanu, da kan far musu a cikin daji, su kashe su su kwashe musu dukiya, da kuma ko su sace su sai an biya kudin fansa kafin su sake su.
” Gwamna Bala ya na nufin, matanen kirki cikin su wanda ba a iya sama musu tsaro ba kan nema ma kan su tsaro ta hanyar mallakar makami. Amma ba wai yana halatta rike bindigogi bane da mahara ke yi.
Giɗaɗo ya kara da cewa kalaman gwamna Bala na yin kira ne ga mutane da masu ruwa da tsaki su rika iya wa bakunan su, maimakon furta kalaman da zai ruruta rashin zaman lafiya a kasar nan, su rika tauna duk abinda za su ce kafin su furta.
Gwamnan Bala yayi kira da yin gargaɗi ga sauran gwamnoni da su rika sara suna duban bakin gatari domin tura fa yana neman ya kai bango game da irin muzguna wa ƴan Arewa da ake yi a wasu jihohin Kasar nan.
Bala ya feɗe biri daga kai har wutsiya inda ya yi kira ga shugabanni su rika iya wa bakunan su, suna yi musu linzami.
” Najeriya kasa ce ta duk ɗan Najeriya, Fulani makiyayi yana da ƴanci da damar ya yi kiwo a duk faɗin kasar nan kuma ya zauna da mutane ba tare da an muzguna masa ba.
” A baya Fulani makiyayi na rike makami idan zai fantsama daji kiwo saboda namun dajin da za su yi far masa, shi kuma ya kare kan sa da dabbobin sa. Zamani ya kawo mu yanzu ba namun daji ba ne kawai makiyayi ke kokarin kare kan su da dabbobin su daga har da barayin shanu. Sai kaga makiyayi an far masa da bindigogi a daji an kashe shi sannan an yi awon gaba da dabbobin sa.
” Wannan shine dalilin da ya sa dole shima Fulani makiyayi ya siya bindiga domin irin wadannan mutane. Ya kare kan sa sannan ya kare dukiyar sa.
” Maganan wai Fulani makiyaya su fice daga dazukan wasu jihohi bai ma taso ba. Dazuka dai na gwamnati ne sannan shi makiyayi dan kasa ne. Ba zai yiwu ka hana shi rayuwa ba sannan kai ba ka yi mishi tanadin inda zai koma ba.
” Muma fa a jihohin mu akwai mutanen jihohin da ake korar mana mutane. Anan jihohin bamu taba cewa don an hana mutanen mu wani abu a can ba su ma na nan dole su tashi su koma garuruwan su.
” Gaskiya ɗaya ce kuma ita ce gwamnan Benuwai Emmanuel Ortom shine ya fara ballo wannan matsala da aka shiga yanzu. Sannan kuma ko a jihohin mu akwai ƴan kabilar sa Tivi da Yarabawa a ko ina tare da mu, ba mu ce musu su koma garuruwansu ba.
Gwamna Bala ya karisa jawabin sa da jinjina wa shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, gwamnan Filato, Simon Lalong wanda ya yaba masa kan yadda yake jagoran kungiyar gwamnonin.