Wani jagora kuma gogarman masu satar mutane a jihar Zamfara, Auwalu Daudawa ya yi sallama da yin garkuwa da hare-hare da yake yi a jihar.
Baya ga shi akwai wasu abokan aikin sa shida da suma sun mika wuya, sannan sun mika wa gwamnati da jami’an tsaro bindigogi kirar AK47 har guda 20.
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ta ruwaito cewa Daudawa ya mika wuya ne a gaban gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle in da ya ce ya ya tuba daga wannan sana’a na satar mutane a jihar.
A jawabin da yayi a wajen yi wa Daudawa da makarraban sa wankan tsarki, gwamna Matawalle ya gode masa da sauran abokan aikin sa da suka mika wuya suka tuba sannan suka ajiye mika wa jami’an tsaro makaman su.
” Wannan abu yayi mana farin ciki, za mu ci gaba da tattaunawa da neman sulhu a tsakanin mu da ‘yan bindiga da suka addabi jihar. Wannan shina abinda muka saka a gaba kuma za mu ci gaba da yi. Muna rokon sa da ya hada kai da gwamnati ya taya mu rokon sauran ‘yan bindigan su hakura da wannan sana’a su mika wuya suma.
” A ce wai yau an samu dan bindiga guda daya da zai mika bindigogi har 20 kuma manya abin murna ne matuka.