Gogarman korar Fulani Makiyaya daga yankin Yarabawa ya fara aiki gadan-gadan

0

Ɗan gwagwarmayar korar Fulani Makiyaya daga yankin Yarabawa Sunday Igboho ya dira jihar Ogun domin fara aikin fatattakar Fulani dake zaune a yankin Yarabawa wato jihohin Kudu Maso Yamma.

Idan ba a manta Sunday Ighobo wanda shine jagoran wannan tafiya ya dira garin Ogun da yammacin Litinin inda ya gana da manema labarai.

A jawabin sa Sunday ya ce ” Daga nan za mu dira kauyen Yewa inda Fulani ke a zaune mu fatattake su su fice mana daga jiha da yankin mu gaba daya.

” Mu zo garin Abeokuta ne domin mu taimaki yan uwan mu Yarabawa don gamawa da Fulani Makiyaya. Ko suna so ko basu so dole Fulani Makiyaya su fice daga wannan yankin na mu. Ba za mu ɗaga musu kafa ba. Za mu bisu duk inda suke mu fatattake su domin yanzu a shirye muke.

Bayan haka ya godewa wa shugabannin yankin Yarabawa, Sarakuna, gwamnoni da manyan yankin bisa goyon baya da suka bashi tun bayan da ya bijiro da wannan aiki na fatattakar Fulani Makiyaya a yankin Yarabawa.

” Har yanzu banga wani jagora ko shugaba dan asalin yankin mu da baya goyon bayan wannan gwagwarmaya da na saka a gaba.

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Ondo ta dakatar da kiwon a fadin jihar da dare, sannan kuma da hana kiwo a wasu dazukan dake jihar.

Share.

game da Author