Gobara ta babbake Katafaren ginin Bababa dake Bauchi

0

A cikin daren Juma’a ne ibtila’in gobara ya babbake katafaren ginin rukunin shaguna mafi girma da ke cikin garin Bauchi wanda ake kira Bababa.

Gobarar ta babbake wani bangare na ginin dake dauke da shaguna masu yawa wadanda ke cike da kayan siyarwa na jama’a.

Har zuwa wannan lokaci da ake rubuta wannan labari, wutar na ci gaba hayayyaka yana kama wasu bangarorin kataren rukunin shagunan dake ginin Bababa.

Shugaban ma’aukatan fadar gwamnatin jihar Bauchi, Ladan Salihu, wanda ya ruwaito abinda ke faruwa a wannan wuri kai tsaye ya ce ma’aikatan hukumar kashe gobara na kokarin kashe gobarar.

Bisa ga bidiyo da ya saka a shafinsa ta Facebook an tafka asara mai dinbin yawa a wannan gobara sannan kuma ya mutane makin zagaye da kasuwar suna zuba wa ikon Allah ido yadda gobarar ke balbali sai ci yake duk da ruwa da ma’aikata ke kwarara mai.

Wasu da wutan bai kai ga shagunan su ba na kokarin kwashe kayan shagunan mai makon su rasa komai.

Share.

game da Author