Gwamnan jihar Kaduna ya gargaɗi mazauna garin maraban Jos cewa duk wanda ya bari babbar motan ɗaukan kaya ko mai ta yada zango a gaban gidansa, gwamnati za ta rusa wannan gida sannan ta ci taran wannan mota, tara mai yawan gaske.
Gwamna El-Rufai yayi wa mutane wannan kasheji ne da kakkausar murya inda ya ke nuna fushin sa ga yadda direbobin manyan mota ke karya dokar gwamnati duk da kokarin gina musu wajen ajiye motocin su idan suka zo wannan gari.
Gwamnatin jihar Kaduna ta gina wa manyan motoci da ke yada zango a Maraban Jos wurin ajiye motocin su amma direbobin sun ki shiga wannan gareji suna ci gaba da ajiye motocin su a bakin titi wabda yana cike da haɗarin gaske.
A lokutta da dama ana samun yawaitar haɗarurruka a wannan hanya a dalilin wadannan motoci da suke yada zango a garin maraban Jos.
” Saɓa doka ne a baka fili ka gina gida amma ka maida gidan wajen ajiye manyan motoci. Duk mai gidan da bai hana haka a gaban gidan sa ba, toh za mu dawo mu rusa gidan domin ya karya dokar da ta bashi damar gina gida ne kawai ba wajen tara manyan motoci ba.
Discussion about this post