Ganduje zai kashe naira biliyan daya don gyaran magudanar ruwa da sanya wutan lantarki a titunan Kano

0

Gwamnatin jihar Kano ta ware naira biliyan daya domin sanya wutan lantarki a titunan Kano da gyaran magudanan ruwa a fadin jihar.

Kakakin hukumar kula da filaye na jihar Auwal Ado ya sanar da haka a wani takarda da aka raba wa manema labarai ranar Litini.

Ado ya ce za a gina magudanar ruwa a karamar hukumar Bichi Wanda zai taso daga Kwatas din Sanka dake Kofar Sidi Ahmed, zuwa Kofar Dan Iya Aminu zuwa Kofar Wambai a Bichi.

Sannan a saka wutan lantarki a titin dake France-Zungeru da Lamido road.

Babban sakataren hukumar Muhammad Yusuf ne ya sa hannu a madadin gwamnatin jihar Kano a takardar yarjejeniyar kwangilar, sannan Aliyu Ibrahim, ya saka hannu a madadin kamfanin Tiamin Multi-Service Global Limited wanda zai yi aikin.

Idan ba a manta a makon jiya gwamnatin Tarayya ta sa hannu da kulla yarjejeniyar gina karamar tashar wutar lantarki mai zaman kan ta, mai karfin migawat 25 a Kano.

Za a gina wannan karamar tasha ne domin amfanin masana’antun da ke bangaren Kasuwancin da babu Talala da Haraji wato ‘Kano Free Trade Zone (KFTZ).

Wutar wadda wani kamfani mai zaman kan sa ce zai gina tashar ta, ana sa ranar daga zanar da za a fara ginin, za a dauki watanni 11 kacal a kammala aikin baki daya.

Share.

game da Author