Kakakin ma’aikatar shari’a Zainab Baba-Santali ta bayyana cewa babban kotu dake Dutse jihar Jigawa ta yanke wa wani matashi mai shekaru 27 hukuncin daurin rai-da-rai bayan ta kama Shi da laifin yi wa ‘yar shekara 11 fyade.
Zainab ta Kuma ce kotun ta yanke wa wani matashi mai shekaru 21 hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru 21 da shima aka kama da kafin aikata fyade.
Sannan kotun ta saki wani da ake zarginsa da aikata fyade bayan masu kara ba su iya kawo kwarararn hujjoji da zai tabbatar da ya aikata laifin ba.
Zainab ta ce Suleiman Ahmed Mai shekaru 27 mazaunin kauyen Lutai dake Birnin Kudu ne, ya bi ta kan wannan yarinya mai shekaru 11 a wani kangon gini dake garin Babaldu ranar 15 ga Maris 2020.
Ta ce shaidu hudu wanda a ciki akwai kawayan yarinyar da aka yi wa fyaden sun bayyana a kotun cewa sun ga Ahmed a lokacin da yake lallabar yarinyar zuwa wani kangon gini.
Kawayen sun ce sun bi sawun Ahmed zuwa kangon ginin inda suka iske shi yana lalata da kawar su.
Bayan haka Zainab ta ce kotun ta kuma daure Adamu Ali mai shekaru 21 a kurkuku na tsawon shekara 21 bayan an kama shi da laifin yi wa ‘yar shekara 9 fyade.
Zainab ta ce alkalin kotun Ubale ya yanke wannan hukunci ne bisa ga bayanan da shaidu hudu da aka gabatar a kotun suka bada.
Zainab ta ce makarantar da yarinyar ke zuwa ne suka kai da kara a ofishin ‘yan sanda bayan sun ga yarinyar na dangal-dangal bata da lafiya.