Fadar Shugaban Kasa ta jaddada cewa tsallake siradin matsin tattalin arziki, wato ‘economic recession’ da Najeriya ta yi kwanan nan, ya nuna tabbar Shirin Bunkasa Tattalin Arziki da Gwamnatin Tarayya ta bijiro da shi, ya na aiki matuka.
Kakakin Yada Labarai na Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka, tare da cewa ‘yan Najeriya su zuba ido su ci gaba da ganin yadda tattalin arzkikin Najriya zai kara bunkasa.
Akande ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya ke yi wa kafafen yada labarai karin haske dangane da yadda Karfin Tattalin Arzikin Cikin Gida na Najeriya ya karu a watanni uku na karshen shekarar 2021.
Cikin watan Yuni ne dai Shugaba Muhammadu Buhari tare da Majalisar Zartaswa su ka amince da Shirin Bunkasa Tattalin Arziki, ko kuma ‘Economic Sustainablity Plan’, wanda aka damka shirin a hannun Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, domin tabbatar da cewa ya jagoranci shirin ta yadda za a samu gagarimar nasara.
Shi dai wannan shiri ya ta’allaka ne wajen hana sake afkawa cikin matsin tattalin arziki, ta hanyar danna kudade a hannun ‘yan Najeriya, tun bayan kuncin rayuwar da aka fuskanta bayan barkewar cutar korona.
Najeriya dai ta tsallake siradin matsin tattalin arziki a cikin watanni uku na karshen shekarar 2020.
Cikin watan Yuni ne dai Shugaba Muhammadu Buhari tare da Majalisar Zartaswa su ka amince da Shirin Bunkasa Tattalin Arziki, ko kuma ‘Economic Sustainablity Plan’, wanda aka damka shirin a hannun Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, domin tabbatar da cewa ya jagoranci shirin ta yadda za a samu gagarimar nasara.
Discussion about this post