Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da fasinjojin babbar motar gwamnati na jihar Neja sun yi ikirarin cewa lallai sai gwamnati ta biya su naira miliyan 500 kafin su saki wadannan mutane.
A bidiyo da maharan suka fitar ranar Talata sun ce ko ba wadannan ba kawai, akwai wasu mutanen da dama da suka yi garkuwa da su a cikin dajin.
An nuno mata da yara kanana suna zabga kuka suna rokon gwamnati ta kawo musu ɗauki.
Maharan sun rika tsorata mutanen da suka yi garkuwa da su da bindigogi da kuma bindiga mai lizami na harbo jirgi daga sama.
An yi garkuwa da Ɗaliban makarantar Sakandaren Kagara
Ƴan bindiga sun sace dalibai da dama a makarantar Sakandaren Kwana dake Kagara, Jihar Neja.
PRNigeria ta ruwaito cewa maharan sun dira makarantar Kagara cikin dare inda suka fi karfin jami’an tsaron dake gadin makarantar sannan suka kutsa cikin makarantar suka yi awon gaba da ɗalibai da dama.
Sanata Shehu Sani ya ce shugaban makarantar ya tabbatar masa da aukuwar wannan abin tashin hankali.
PRNigeria ta ruwaito cewa wasu ɗaliban sun gudu a lokacin da maharan suka tarkata su suka wuce da su, kuma maharan sun isa makarantar ne sanye da kayan sojoji.
Wannan dauke ɗalibai da aka yi ya zo watanni uku bayan an sako daliban makarantar Kankara jihar Katsina.