Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa bangaren noma a Najeriya ya samu bunkasa da kashi 2.17a cikin 2020.
NBS ta ce a cikin shekarar 2019, karin kashi 2.36 aka samu. Sai kuma cikin 2018 aka samu karin kashi 2.12 kadai. Wannan ya nuna a shekarar 2020 an fi shekaru biyu na baya da suka gabata samun albarkar noma kenan.
Rahoton wanda aka fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa harkar noma a 2020 ta bunkasa sosai a cikin watanni uku na karshen shekara. Kuma a wadannan watanni ne tattalin arzikin cikin gida ya karu da kashi 26.21 baki daya.
Rahoton ya kara bayyana cewa a cikin wadannan watanni uku na kashen shekarar 2020 ne tattalin arzikin Najeriya ya tsallake siradin kuncin rayuwar da ya afka.
Wannan fita daga matsin tattalin arziki kuwa na da nasaba da bude kofar kullen korona da aka yi wa jama’a na tsawon watanni.
Tattalin arzikin Najeriya ya shiga jula-jula cikin watannin shida, bakwai da takwas na shekarar 2020, wanda ya yi sanadiyyar Najeriya afkawa cikin matsin tattalin arziki da kuncin rayuwa karo na biyu, a cikin shekaru biyar.
Tattalin arzikin Najeriya ta wancan lokacin ya dan tauye da kashi1.92, fiye da yadda Bankin Bada Lamuni na duniya, IMF ya yi kintace da kirdado kan Najeriya.
Rahoton NBS ya nuna cewa bangaren kayan abinci, kiwon dabbobi, kula da dazuka da kuma bunkasa sana’ar kiwon kifaye ne su ka cicciba tattalin arziki a fannin noma har ya samu waraka da nasibi cikin 2020.
An samu albarkar kayan gona na bangaren abinci sosai a shekarar 2020, daga su kuma sainsana’ar kiwon kifi su ne su ka kara wa fannin noma albarka sosai.