Fani- Kayode ya wancakalar da PDP, ya dawo APC – In ji Yahaya Bello

0

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana wa dandazon magoya bayan APC a jihar Kogi cewa tsohon ministan sufurin jiragen Sama na Kasa, Femi Fani-Kayode ya dawo jam’iyyar APC.

Yahaya Bello ya bayyana cewa dama can da shi Femi aka aza tubalin kafa jam’iyyar APC kafin saɓani ya sa ya fice daga jam’iyyar ya koma wata jam’iyyar.

” Ina so in tabbatar muku yau cewa fitaccen ɗan siyasa Fani-Kayode ya dawo gida, wato APC, kuma muna maraba da shi.

Idan ba a manta ba an rika saka hotunan gwamna Yahaya da shugaban jam’iyyar APC, gwamnan Yobe, Mala Buni da Fani-Kayode a shafukan yanar gizo a lokacin da ake tartaunawa.

Fani Kayode na daga cikin wadanda suke yin tsananin adawa ga jam’ iyyar APC tun bayan kasa PDP da ta yi a zaben 2015.

Sannan kuma da nuna tsananin kiyayyarsa ga musamman yankin Arewa wand wasu ke gani bai taba fadin alkhairi ga gwamnatin Buhari da yankin Arewa ba.

Share.

game da Author