Babban Joji a Babbar Kotun Jihar Delta, Mai Shari’a Anthony Okorodas, ya fito fili a karon farko ya bayyana yadda gwajin-’yar-kure na DNA ya tabbatar masa cewa ’ya’ya uku daga da matar sa ta haifa a gidan sa kafin su rabu, wani kato ne ya yi cikin ba shi ba.
Okorodas dai ya zama Mai Shari’a a Babbar Kotun Jihar Delta cikin 2018. Ya yi wannan ikirari a cikin wata muhimmiyar sanarwa da ya itar a ranar Alhamis, 28 Ga Janairu, 2021.
Mai Shari’a Okorodas ya fitar da sanarwar cewa tsohuwar matar sa mai suna Celia, ta arce daga gidan sa tun karamin yaron su ya na da shekaru shida da haihuwa. Amma a yanzu yaron shekarar sa 17.
Ya ce shi da matar sa da ya ke aure a yanzu bayan waccan uwar yaran ta gudu ne su ke daukar dawainiyar karatun yaran uku, wadanda bai taba tunanin wani kato ne ya rika dirka mata ciki duk ta haife su ba, sai a baya-bayan nan da gwajin DNA ya tabbatar.
Okorodas ya ce ya gano hakan ne tun a cikin watan Afrilu, 2020, lokacin zaman kullen korona a gida.
Sai dai kuma ya ce bai samu sararin tabbatar da ikirarin ba, sai cikin watan Agusta, 2020.
ya ce tsohuwar matar ita ma lauya ce, wato Barista Celia Juliet Otokoto, daga Karamar Hukumar Yenagoa, cikin Jihar Bayelsa.
“Bana shekaru 11 kenan da mu ka rabu, kuma igiyar aure a tsakanin mu ta tsinke.”
“Wata rana ana zaman kullen korona cikin Afirilu, 2020, wani da ba zan bayyana sunan sa ba, saboda dalili na tsaro ya sanar da ni gaskiyar magana cewa ‘ya’yan da tsohuwar mata ta ta haifa a gida na su uku, duk wani kato ne ya yi mata cikin, ba ni ba.’’
“To saboda kullen korona ban samu damar gudanar da gwajin DNA ba, sai cikin Agusta, 2020.
“Gwajin DNA ya fito cikin watan Satumba, 2020, tare da tabbacin cewa ba ni ba ne na yi cikin yaran su uku, wani kato ne ya yi mata cikin.”
Bayan sakamakon gwajin DNA ya fito, Okorondos ya kira taron bangaren iyayen sa da bangaren iyayen tsohuwar matar sa. kuma ya baje masu a faifai sakamakon gwajin da DNA ya tabbatar a kan yaran uku.
“Duk da ta hakikice cewa ni ne na yi cikin, amma kuma daga baya ta ce wani ne ya yi cikin yaron farko a lokacin auren mu.”
“Saboda rashin kunya, sai Celia ta ce wai na yi gwajin DNA a kan sauran yaran biyu. Bayan kwana kadan sakamako ya sake fitowa, su ma din dai kamar yadda sakamakon farko ya nuna, wani kato ne ya dirka mata cikunnan, ba ni ba.
“Wannan abin kwatagwalci ya janyo min damuwa, dimuwa da shiga halin kaka-ni-ka-yi. Kamar yadda mata ta ta yanzu da su ma yaran su ka shiga cikin halin matsanancin damuwa.”
“Amma yara na hudu da mata ta da na ke aure a yanzu, DNA ya tabbatar da duk ni ne na yi cikin su.”
Okorodas ya ce saboda tsoro da firgita kan abin da ya faru, sai ya gudanar da gwajin DNA a kan sauran ‘ya’yan sa hudu da ya haifa tare da matar da ya ke aure a yanzu.
Aka gwada, kuma aka tabbatar cewa shi ne ya yi cikin su ba wani kato ba, kamar irin yadda wani kato ya haifi yara uku da tsohuwar matar sa, kafin su rabu.
‘Ba Zan Daina Kula Da Yaran Da Wani Kato Ya Haifa Da Tsohuwar Mata Ta Ba –Babban Mai Shari’a:
Okorodas ya ce, amma duk da fallasar da gwajin DNA ya yi, hakan ba zai hana shi ci gaba da kula da daukar dawainiyar karatun ‘ya’yan wadanda ta haifa da wani kato a gidan sa ba.
Ya ce tun bayan rabuwar sa matar, shekaru 11 da suka gabata, shi da matar sa ta yanzu ke kula da yaran da matar ta haifa da wani kato. Yanzu haka ma biyu daga cikin su na jami’a.