Duk mai ‘adaidaita’ sai ya yi rajista da biyan naira 100 duk rana kafin ya yi aiki a Kano – Gwamnatin Ganduje

0

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin ba za ta lamunta wa duk wani mai tuka keken adaidaita sahu ba muddiun ba zai biya harajin naira 100 duk wata ba.

Wannan dokar biyan haraji da aka kirkiro a jihar Kano ya kawo cikas da rudani a harkar sufuri da jigilar jama’a a jihar.

Sai dai kuma duk da wannan matsaloli da jama’a suka fada ciki gwamnati ta ce ba zata lamunta wa masu keke napep din ba muddun ba za su bi umarnin gwamnati ba na biyanharajin naira 100 duk rana ba.

Kungiyoyin masu tuka adaidai ta sun shiga yajin aiki a jihar inda lashi takobin ci gaba da zama a gida har sai gwamnati ta sauya ra’ayinta na kakaba musu wannan haraji.

Shugaban kungiyar masu tuka keke nape na jihar Kano, Sani Dankoli, ya roki gwamnati ta janye wannan sabon karaji domin ba kungiyar daman tattaunawa da ‘ya’yan kungiyar tukunna.

Shugaban hukumar kula da bin dokokin hanya na jihar Kano, Baffa Babba-Dan’agundi, ya bayyana cewa sai da gwamnati ta tattauna da shugabannin kungiyar matuka keke napep din kafin ta bijiro da wannan haraji.

Gwamnatin Kano ta ce ba za ta yi ami ta lashe ba game da harajin ‘yan adaidaita. ” Gwamnati na so ta gyara fasalin yadda ake aiki da baburan ne a jihar. Wasu da dama basu da lasisi ma, kuma wasun su ana amfani da su wajen yin garkuwa da mutane. Gwamnati za ta gyara fasalin yadda ake aiki da su ne.

Tuni har gwamnati ta baza manyan motocin mallakar jihar domin jigilar mutane zuwa wuraren aikin su.

Share.

game da Author