Dokar Najeriya ta ba kowa damar zama a inda ya ke so, bai kamata a zuba wa wasu ido suna muzguna wa wasu ba – Gargadin El-Rufai

0

El-Rufai ya gargadi mutane da gwamnatocin jihohin kasar nan su rika sara suna duban bakin gatari kan ingiza mutane su tada rikici a inda suke zaune.

Gwamna El-Rufai yayi wannan kira da gargadi ne a wata doguwar jawabi da yayi wa mutanen jihar Kaduna ranar Laraba in da ya ce gwamnatin sa ba zata yi na’am na yinkurin da wasu a kasar nan ke yi na neman tada zaune tsaye ba.

El-Rufai ya ce jihar Kaduna ta yi fama da irin wadannan rikice-rikice na son rai da nuna kiyayya a tsakanin mazaunan jihar.

Ya yi gargadi ga wadanda ke saka wani bidiyo da ke nuna kashe-kashen wata kabila a wasu yankunan kasar nan yana mai cewa wannan bidiyo bai kamata a rika yada shi domin zai iya ingiza mutane su dau mataki a hannun su wanda ba shi ne kasar nan ke bukata a wannan lokaci da muke ciki ba.

” Da yawa daga cikin mutanen jihar Kaduna sun tambaye ni ko na san inda aka dauki wannan bidiyo dake nuna yadda ake kone-kone da tashin hankalin ‘yan wasu kabila a wani yankin kasar nan, domin babu abin da irin wannan bidiyo zai haifar illa mummunar tashin hankali a kasar nan idan ba a yi gaggawar jawo hankalin shugabannin wadannan yankuna da ake zaton a can wuraren su aka dauki wannan bidiyo.

” A madadin Gwamnatin Jihar Kaduna, ina kira ga dukkan ‘yan Najeriya mazauna Jihar mu da su girmama doka da oda da kuma ‘yancin kowane dan kasa na rayuwa da zama cikin aminci da tsaro a duk inda suke zaune ko aiki. Ina kira ga takwarorina da ke mulki a wasu Jihohi a cikin kasar nan da su yi irin wadannan jawabai na yin gargadi da ja wa mutanen jihohin su kunne, kuma su yi tir da wadannan hare-hare da ake yi.

” Dole ne fa gwamnatoci su tashi tsaye haikan domin tabbatar da kowa ya kiyaye bin doka da oda sannan kuma a hukunta duk wanda ya karya doka ko shi waye kuwa a kasar nan. Bai kamata a bari ana tada hankulan mutane na babu gaira babu dalili ba. Suma shugabannin addinai dole su tashi tsaye wajen jan kunnen mabiyan su da yi musu gargadi.

” Kada mu bari ayyukan wasu tsiraru ‘yan ta’adda ya tarwatsa hadin kan da muke da shi a kasar nan. Bai kamata a bari wasu ‘yan ta’adda su yi wa doka hawan kawara ba, suna bi suna cin mutunci wadanda basu ji ba basu gani ba sannan a zuba musu ido sai yadda suka yi a kasar nan.

Gwamnan yayi kira ga majalisar kasa da ta gagguta tattauna batun kafa ‘yan sandan jihohi a kasar nan yana mai cewa yin haka zai kawo sauki matuka da tsaro a kasar nan. Sannan kuma gwamnan ya tunatar da mutane irin kokarin da gwamnatin sa ta wajen sakawa a kama wasu da suka nemi wai wasu kabila ta fice daga jihar Kaduna a 2017.

Gwamnan ya ce an yi haka ne domin a tuna sar duk wani mazaunin jihar cewa Najeriya ta kowa da Kowa ne dan kasa kuma za ka iya zama a duk inda kake so ba tare da an tsangwameka ko an muzguna maka ba.

Share.

game da Author