Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya kori kwamishinan kiwon lafiyar jihar Salisu Kwaya-Bura ranar Talata.
Bisa ga sanarwar haka da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yadda labarai Isa Gusau ya yi a wani takarda da aka raba wa manema labarai ya ce gwamnati bata fadi dalili kai tsaye wai shine abinda ya sa ta sallami kwamishinan.
Kafin a sallami kwamishinan daga aiki Kwaya-Bura shine sakataren kwamitin dakile yaduwar cutar korona na jihar sannan a mafi yawan lokutta shine yake nuna iyayi game da ayyukan kwamitin duk da cewa mataimakin gwamnan Umar Kadafur ne shugaban kwamitin.
Gusau ya ce tuni har gwamna Zulum ya maya gurbin Kwaya-Bura da Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati kuma masanin magani da ya kware a yin bincike kan cutar daji Isa Hussani Marte.
Koran Kwaya-Bura daga aiki.
Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an kori Kwaya-Bura daga aiki ne saboda yadda ya yake nuna son kai da bada fifiko ga wani yankin jihar maimakon yi wa mutanen jihar gaba daya aiki.
A kwanakin baya gwamna Zulum ya dauki ma’aikatan lafiya 694 a fadin jihar wanda daga baya aka gano cewa Kwamishinan Lafiya Kwaya-Bura ya yi son kai inda ya rika daukar mutanen sa kawai yan kuma gari daya.
Wata majiyar ta kuma bayyana wa gidan jaridar nan cewa akwai yiwuwar an sallami Kwaya-Bura daga aiki ne saboda sama da fadi da aka yi da wasu makudan kudaden ayyukan Korona a jihar.
Sai dai majiyar bata tabbatar mana da cewa ko Kwaya-Bura na daga cikin wadanda har yanzu ba a wanke su daga zargin satar kudaden ba.
Kwaya Bura ya lokaci yayi na barin aikin sa kawai shine ya sa aka sallameshi.
Discussion about this post