A taron da kwamitin PTF ta yi da manema labarai ranar Litini shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Faisal Shu’aib ya yi karin haske kan dalilin da ya sa ba za a yi wa kananan yara allurar rigakafin cutar korona ba.
Shu’aib ya ce dama tun a farko ba a tsara yin maganin rigakafin Korona da yara ba. Bayan haka an gano cewa idan aka dirka wa yaro karami rigakafin zai iya yi masa lahani.
Ya ce a dalilin haka ya sa ba a yin gwajin ingancin maganin a jikin yara kananan ba.
“A lokacin da ake yin gwajin inganci da sahinancin maganin rigakafin an gwada shi ne a jikin yara masu shekaru 16 zuwa sama.
“Masana kimiyyar hada magunguna sun ce dalilin yin haka shine ganin cutar korona ta fi kama manya ko masu fama da cututtuka a jikin su ne da tsofaffi.
“A yanzu haka masana kimiyya na gudanar da bincike domin gano ko menene illar da maganin rigakafin Korona zai iya kawo wa yara.
A makon da ya gabata PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin cewa Najeriya za ta yi wa mutum miliyan 109 allurar rigakafin cutar korona daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.
Gwamnati na sa ran karban kwalaben maganin rigakafin miliyan 57 daga AVATT da COVAX da kuma wasu miliyan 1.5 da 100,000 wanda kamfanin MTN da kasar India suka baiwa Najeriya gudunmawa wanda za a yi amfani da su wajen yi wa wadanda suka dara shekaru 18 allurar rigakafin a kasar nan.
ita.