Dalilin da ya sa na karkata ga a kirkiro ‘yan sandan Jihohi – El-Rufai

0

Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti da takwaran sa Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, kirkiro ’yan sandan jihohi da kuma karfafa kotuna a jihohi ne ai kara zama sanadin mahance matsalar rashin tsaro a fadin kasar nan.

Gwamnoni sun bayan nan haka ne a wani taron kai-daga-nesa, wato ‘virtual meeting’ a ranar Asabar, inda su ka ce a karkasa karfin kotuna daga tarayya zuwa cikin jihohi tare da kirkiro ’yan sandan jihohi.

PREMIUM TIMES ta sa-ido a kan taron mai suna “Dabaru da Hikimomin Yadda Za a Hana Najeriya Durkushewa”.

El-Rufai ya ce bai wa kowace jiha ikon kafa na ta ’yan sanda zai tseratar da Najeriya daga durkushewa saboda rashin tsaro.

Ya kara da cewa an dade ana ruwa kasa ta na shanyewa. Ma’ana, kafa ’yan sanda daga gwamnatin tarayya kuma a karkashin gwamnatin tarayya, amma abin bai kawar da matsalar tsaro ba.

‘A Bar Wa Jihohi Masu Man Fetur Ikon Man Su Kawai’ –El-Rufai

“Abu na biyu, ina ganin cewa a bar wa jihohin da ke da arzikin danyen man fetur ikon albarkatun man su kawai, kamar yadda jihohi ke da iko da kasa ko filaye a kowace jihar kasar nan. Amma sai dai kawai za su rika biyan gwamnatin tarayya wani kaso daga arzikin kudaden danyen fetur din na su, a matsayin haraji.”

El-Rufai ya ce akwai bukatar haka idan za a yi wa dokar Najeriya kwaskwarima domin a tabbatar da wannan batu.

“Abu na uku shi ne a rage karfin kotuna daga tarayya zuwa jihohi.”

‘Gwamna Ba Shi Da Iko Da ’Yan Sandan Najeriya’:

” Cikin shekaru biyar da rabi din nan ina gwamna, an yi Kwamishinan ’Yan Sanda 8 a Jihar Kaduna. Haka kawai sai dai na ga an canja wannan, an kawo wancan, ba shawarar ake yi da ni ba.

“Shin ta yaya za a iya tsare jiha da al’ummar da ke cikin ta, idan duk bayan wata takwas sai an canja kwamishinan ‘yan sanda?

“Gwamna ba shi da iko da ‘yan sanda, saboda a karkashin gwamnatin tarayya su ke. Kwamishinan ’Yan Sanda babu ruwan sa da daukar umarni daga Gwamna. Eh, za ka iya kiran sa ka ce ga wata matsala. Amma da ya kira Sufeto Janar ya sanar da shi, kuma ya ce, ‘kai rabu da shi, to shikenan an bar gwamna tsaye a tasha.”

Shi ma Gwamna Fayemi duk dai zancen na sa kudan daya ne da na El-Rufai. Sai dai shi ya fadada jawabin sa da cewa Najeriya na bukatar shugabanni na kwarai kafin a magance matsalar tsaro a kasar nan.

Ya kuma rika kawo misalan matsalolin rashin tsaron da su ka dabaibaye kasar nan na baya-bayan nan da ya ce abin tsoro ne matuka.

Share.

game da Author